Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D
Gabatarwa
Zaman lafiya a cikin gida shine ginshiƙin zaman lafiyar al’umma bakiɗaya. Duk wata al’umma da ke da iyalai masu tsari da bin doka, tana da damar samun cigaba mai ɗorewa. A gefe guda kuma, rashin tsari da doka a gida yana haifar da rikice-rikice, rashin ladabi da lalacewar tarbiyya.
Masana ilimin zamantakewa sun bayyana cewa, gida shine “makarantar farko” da ke koyar da mutum yadda zai rayu a cikin al’umma. Saboda haka, doka da ka’ida a gida suna da muhimmanci wajen tsara rayuwar yara da manya.
Ma’anar doka da ƙa’ida a gida
Doka da ka’ida a gida na nufin tsarin rayuwa da aka shimfiɗa domin tafiyar da harkokin iyali cikin tsari da adalci. Wannan ya haɗa da:
ƙa’idojin tarbiyya
Tsarin ayyuka na yau da kullum
Haƙƙoƙi da alhakin kowane ɗan gida
Masana irin su Émile Durkheim sun bayyana cewa doka tana da muhimmanci wajen daidaita zamantakewar jama’a, domin tana hana rikici da rashin tsari.
Muhimmancin doka da ƙa’ida a gida
1. Tabbatar da zaman lafiya
Doka tana rage sabani a tsakanin ‘yan gida. Misali, idan an kafa cewa kowa yana da lokacin aikinsa (kamar tsaftace gida ko karatu), to za a rage gardama da zargi.
2. Gina tarbiyya mai kyau
A cewar A. B. Fafunwa a cikin History of Education in Nigeria, tarbiyya mai kyau tana farawa ne daga gida, kuma dole ne ta kasance cikin tsari da ka’ida.
3. Koyar da dogaro da kai da sanin muhimmancin lokaci
Doka tana koya wa yara su ɗauki nauyin kansu. Misali Yaro ya san lokacin tashi makaranta,ya san lokacin yin aikin gida, ya san abin da ake sa ran zai yi.
4. Samar da adalci
Idan doka ta kasance iri ɗaya ga kowa, to za a guji nuna son kai. Wannan yana koya wa yara darasin adalci tun suna ƙanana. Haka nan duk lokacin da suka girma za su kasance masu adalci a cikin abokansu ko a cikin iyalansu ko kuma a wani muƙami da suka dafa.
Hujjoji daga addinin musulunci
Allah (SWT) Ya ce: “Lallai Allah yana umurni da adalci da kyautatawa…”
(Surat An-Nahl: 90) Annabi (SAW) ya ce: “Kowannenku makiyayi ne, kuma kowannenku za a tambaye shi abin da ya kula da shi.” (An rawaito a cikin Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim) Wannan yana nuna cewa iyaye suna da alhakin kafa tsari da doka a gida.
Illolin rashin doka a gida
1. Rikice-rikice a iyali
Idan babu tsarin raba aiki, yara na iya gardama kan wa zai yi wane aiki. Haka idan iyaye ba sa gindaya doka a wasu al’amura a tsakanin iyalansu da ya zama wajibi kowa ya bi su sai ya kasance yaran sun tashi ba doka.
2. Lalacewar tarbiyya
Yaro da bai taso cikin tsari ba, zai iya girma yana raina doka a makaranta da al’umma. Haka ko a hanya zai karya doka ba tare da san illar hakan ba akansa ko akan wani.
3. Rashin girmamawa
Idan yara ba su saba da doka ba, za su iya raina iyaye da manya. Haka ba za su bi malamai da dokokin makaranta ba za su tashi ba tsari.
4. Matsaloli a gaba
Masana sun nuna cewa yara da suka taso ba tare da tsari ba sukan fi fadawa cikin laifuka ko matsalolin rayuwa. A kan fi saurin yaudararsu su faɗa wani mummunan hali.
Yadda ake kafa doka mai inganci a gida
1. Tsari mai sauƙin fahimta
Doka ta kasance a sarari, ba mai rikitarwa ba. Kuma daidai wadda kowa zai iya bi musamman ga yara da suke tasowa.
2. Adalci wajen aiwatarwa
Ba a fifita wani yaro akan wani. Haka uwa da uba duka su kasance suna bin wannan dokar da sauran yaransu ba a tsaya akan wasu wasu kuma su yi abin da suka ga dam aba. Kada a nuna son kai tsakanin wani da wani a cikin ‘ya’ya.
3. La’akari da shekaru
Doka ta dace da shekarun yara. Kowanne ɗa akwai abin da zai iya daidai da shekarunsa.
4. Amfani da ladabi da hikima
A guji tsautsauran ra’ayi da kafiya. Iyaye su zama masu sassautawa da tausayawa da ƙauna da rarrashi da lafazi mai taushi.
Ra’ayin masana kan muhimmancin doka
Ibn Khaldun a cikin Muƙaddimah ya bayyana cewa al’umma ba za ta daɗe ba sai da tsari da doka, domin su ne ke tabbatar da zaman lafiya da cigaba. Haka kuma, Imam Al-Ghazali a cikin Ihya Ulum al-Din ya jaddada cewa tarbiyya ba ta cika sai an haɗa ta da tsari da ladabi.
Tasirin doka a gida ga al’umma
Gida shi ne tushen al’umma. Idan gida yana da tsari to ana samun ‘ya’ya masu tarbiyya, ana rage aikata laifi, ana samun zaman lafiya a al’umma. Misali Yaron da ya saba da bin doka a gida, zai bi doka a makaranta da wurin aiki.
Kammalawa
Doka da ƙa’ida su ne ginshiƙan zaman lafiya a gida. Ba za a iya gina iyali mai kyau ba tare da tsari ba. Saboda haka, ya zama wajibi iyaye su kafa dokoki masu kyau, su kuma tabbatar da ana bin su cikin adalci da hikima domin gina al’umma mai ɗorewa.
Manazarta:
Al-ƙur’ani mai girma
Sahih al-Bukhari
Sahih Muslim
Ihya Ulum al-Din – Imam Al-Ghazali
Muƙaddimah – Ibn Khaldun
History of Education in Nigeria – A. B. Fafunwa
