Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da shugabannin jam’iyyar na ƙasa su fito su fayyace matsayarsu kan zargin cewa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami, ya fice daga APC zuwa jam’iyyar PDP.
Jam’iyyar ta ce har yanzu Pantami cikakken mambanta ne, tana mai cewa babu wata hujja da ke nuna cewa ya kammala tsarin yin murabus kamar yadda kundin tsarin APC ya tanada.
Da yake jawabi ga manema labarai a Gombe ranar Talata, sakataren yaɗa labarai na APC a jihar, Moses Kyari Bolde, ya bayyana cewa kwamitin zartarwa na mazaɓar Pantami ya musanta samun ko tattauna wata takardar murabus daga tsohon ministan.
A cewarsa, mambobi 25 daga cikin 27 na kwamitin sun tabbatar da cewa ba su da masaniya kan wata takardar murabus da ake ikirarin Pantami ya miƙa wa jam’iyyar.
“Sun bayyana cewa batun murabus ɗin ƙirƙirarren labari ne da aka yaɗa ba tare da saninsu ko amincewarsu ba,” in ji Bolde.
Ya ce shugaban APC na mazaɓar Pantami, Alhaji Bala Galda, ya bayyana cewa an ce an karɓi takardar murabus ɗin ne ranar 23 ga Mayu, 2026, duk da cewa an sanya mata ranar 19 ga watan Mayu, kuma wani mutum mai suna Abba Pantami ne ya kai ta.
Bolde ya ƙara da cewa duk ƙoƙarin da aka yi domin samun kwafin takardar bai yi nasara ba, lamarin da ya ƙara haifar da tambayoyi kan sahihancin ikirarin.
Ya ce bisa tanade-tanaden kundin tsarin APC, ƙa’idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da dokar zaɓe, Pantami zai ci gaba da kasancewa mamba a APC har sai an bi dukkan matakan da doka ta shimfiɗa wajen ficewa daga jam’iyya.
Jam’iyyar ta kuma yi watsi da ikirarin da ake cewa Pantami ya bayyana a wata hira da gidan talabijin cewa komawarsa PDP da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna sun samu amincewar shugaba Tinubu.
“Ba mu yarda da wannan ikirari ba. Shugaba Tinubu jagora ne mai kishin APC, wanda a ko da yaushe yake ƙoƙarin kare haɗin kai da muradun jam’iyyar. Saboda haka, yana da wuya a yarda cewa zai amince da wani mataki da zai saɓa wa manufofin jam’iyyar,” in ji Bolde.
Sai dai ya yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa abin da ya bayyana a matsayin nasarorin da ta samu a fannoni daban-daban, ciki har da ayyukan raya ƙasa, tabbatar da zaman lafiya da inganta shugabanci a jihar.
A ƙarshe, APC ta bukaci fadar shugaban ƙasa da shugabannin jam’iyyar na ƙasa su fito fili su bayyana gaskiyar lamarin domin daƙile yaɗuwar bayanan da ba su tabbata ba da kuma kauce wa ruɗar da jama’a.
