
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da buƙatar tsohuwar Ministar Harkokin Jin-ƙai, Sadiya Umar Farouq, na soke izinin kamu da kotun ta bayar a kanta.
Kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie, ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2026, bayan lauyan tsohuwar ministar ya nemi a soke umarnin kama ta da kotun ta bayar tun farko.
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC na tuhumar Sadiya Farouq tare da wasu mutum biyu, Bashir Nura Alkali da Sani Nafiu Mohammed kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi, amfani da ofis wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai dala miliyan 1.3 da kuma naira miliyan 746.7.
Yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya bayyana cewa wadda ake ƙara ta ƙi bayyana a gaban kotu ba tare da wata gamsasshiyar hujja ba, yana mai cewa doka ta baiwa kotu ikon bayar da sammacin kamu idan aka tabbatar wanda ake ƙara bai halarci kotu ba tare da wani dalili ba.
Alƙalin ya ce takardun likita da aka gabatar ba su nuna wani gamsasshen dalilin da zai hana Sadiya Farouq halartar kotu ba, duk da cewa an bayyana tana fama da ciwon gabobi da matsalar zuciya.
A ƙarshe, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Yuli, 2026 domin gurfanar da waɗanda ake tuhuma a gaban kotu akan al’amarin.
