Gwamnatin Katsina ta haramta sayen fetur a jarkoki a faɗin jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnatin jihar katsina ta hana saye,sayarwa da jigilar fetur a jarkoki a fadin jihar domin ta wannan hanya ce a ke karkatar da man zuwa ga ‘yan ta’adda.

Gwamnati ta ɗauki wannan matsayi tare da wasu haramci a taron gaggawa na majalisar tsaro na biyar biyo bayan taɓarɓarewar tsaro a faɗin jihar.

‘Yan kwanakin da suka wuce ‘yan bindigan suka kashe wani tsohon babban jami’in soja , Manjo Janaral Rabe Abubakar da wani babban manomi kuma ɗan kasuwa a ƙaramar hukumar Ɗandume da sauran mutane da dama a sassan jihar katsina.

Gwamnati jihar ta bada umurnin rufe wuraren da ake hada hadan kuɗi na POS da kasuwar chajin waya a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.

Haka kuma gwamnati ta hana zirga zirgan baburan hawa a waɗannan ƙananan hukumomi domin daƙile zirga zirgan ‘yan bindiga a yankunan.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya tabbatar wa alummar jihar cewa kare lafiyar su shine ke kan gaba kuma gwamnati za tayi aiki kafaɗa kafaɗa da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya ya samu a faɗin jihar.

Ya ce gwamnati za ta ladabtar da duk wani da ya saɓa waɗannan doka kan haka ne yayi kira ga al’ummar jihar da su taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar ta hanyar bada bayanai ga jami’an tsaro da zai taimaka masu wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

By ukarofi