Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ
Allah masani, ya sanar da mu cewa:
Q41:53 ““Za Mu nuna musu ayõyinMu a cikin sasanni da kuma cikin rayukansu, har ya bayyana a gare su cewa lalle (Alƙur´ani), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cewa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?”
Wannan aya sama da shekaru 1400 da saukar da ita, kuma tsawon zamunna a kullum Allah na jaddada wa Dan Adam ta hanyoyin kimiyya yadda ikonsa ke wanzuwa a halittu duniyoyi da sammai da kuma a cikin jikinmu. Na kurkusan nan shine tsarin Autophagy wanda Allah ya gina a cikin jikinmu. Wanda sai a kwanan nan kimiyya ta binciko mana.
Masanin kimiyya Dan kasar Japan, Dr Yoshinori Ohsumi, ya sami babbar kyautar kimiyya mafi mahimmanci ta Nobel Prize sakamakon bincikensa wanda ya nuna yadda azumi ke da tasirin inganta lafiya da kawar da manyan cutuka irinsu Cancer, Parkinson’s da Diabetes. Wannan tsari, wanda ake kira da Autophagy, tsari ne da Allah ya gina jikin Dan Adam a kansa.
Abinda ke faruwa shine, idan mutum ya na azumi, sakamakon rashin ci da sha, wanda shi ke samar da kuzari (energy) sai kwayoyin halitta na jiki (cells) su baza ma neman kuzari a cikin jiki. Wato akwai geji na iya tsawon san da ka fara azumi, daga kimanin awa 12 sai hanta ta saki wasu sinadarai (mTOR) wanda za su yi shelar jiki ya fara aikin Autophagy. Daga nan sai kwayoyin halitta na jiki su buga kugen yaki su fantsama farautar kwayoyin halitta masu cuta da matattu su yi ta lakume su. Ta haka sai ya kasance sun zama tamkar wata tsintsiyar shara da za ta share dattin jiki.
Babu wani yanayi da ke bunkasa garkuwar jiki kamar wannan tsari, tare da inganta lafiya da kuma rage wa jiki yanayin saurin tsufa.
Malam Abubakar masanin ƙur’ani da kimiyya ne
