Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Rudewarmu a Arewa, musamman cikin al’ummar Musulmi, idan ka yi masa duba na tsanaki da adalci, za ka dora laifin zuwa ga Malamai (a biyo ni a hankali na bada hujja). Idan mu ka yi la’akari da yadda na ga Shehi Aminu Bello ya yi wani tsokaci cewa idan ana rigima tsakanin talaka da mai kudi sai ka ga ana goyon bayan talaka, haka a tsakanin mata da miji, an fi danganta laifi ga miji, ko tsakanin malami da dalibi, sai a raja’a dalibi ne da kuskure, ko Dan kudu da Dan Arewa, mu goyi bayan ɗan Arewa da sauransu.
Wato ɗabi’ar Dan Adam a kullum ya na da saurin goyon bayan wanda ya ke kallo a matsayin nasa ne ko ya fi kusanci da shi (bias ko solidarity, ko class consciousness). Musulunci ya zo da zummar yakar wannan mummunar dabi’a ta Dan Adam wadda idan ka kalle ta da idon basira, ita ce ruhin kusan kashi 70% da ke haddasa duk matsalolin Dan Adam gaba daya, tsakanin daidaikun mutane ko a dunkule a matsayin al’umma ko kasa. Ita ce babban tarnaki wajen tabbatar da wanzuwar adalci a doron duniya.
Dalilin da ya sa na ce malamai ke da laifi tun asali shine, sun kasa gane cewa wannan dabi’a ita ce tushen matsaloli, kuma dakile ta shine babbar maslaha ga al’umma. Allah ya saukar da aya guda daya wadda aiki da ita a zahiri, nan take zai magance wannan matsala.
“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al´amarinsu. Saboda haka, kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to lallai ne Allah Ya kasance Masani ga abin da kuke aikatawa.”
To, mene ne laifin malamai akai? Za a iya ƙalubalen cewa Malamai dai na karanta wannan Aya da wa’azi da ita tsawon zamunna, to ina laifinsu? Amsar ita ce, gazawar su wajen mahimmantawa da cusa ta a zahirance cikin zukatan al’umma. Bari na baku misali yadda za ku gane abinda nake nufi a bayyane.
Akwai abubuwa kimanin guda uku a musulunci wadanda sakamakon yadda malamai tun asali su ka gina su a aikace cikin dabi’ar musulmi, ba ka bukatar jaddada su ga kowa. Na farko shine Shan giya: duk wani musulmi zaka samu ya yarda da haramcin giya da kaurace mata, idan ma ya na yi to a kyamace ya ke yin ta. Wannan dalili ya sa Musulmi ya fi kowa karancin mashaya giya a Duniya. Sannan sai maganar cin naman Alade: babu wani musulmi da zai doshi alhanzir ko a boye ballantana a zahiri. Ba ka bukatar tunatar da Musulmi game da wannan.
Abu na uku shine cin mushe: shi ma wannan ya biyo sahun wadancan. Duk ukun nan ƙurani ne ya bada hukuncinsu, malamai su ka yada su, su ka jaddada kyamatar su a zahiri da badini, kuma ya shiga zukatan musulmi yadda a tsarin tarbiya, tun mu na Yan kanana iyaye ke cusa mana wannan dabi’ar ta kyamatar wadannan abubuwa yadda muke tasowa tunaninmu ya ginu a kansu.
Ita wannan Aya ta Baƙara, idan ka kalli mahimmancinta a tsarin rayuwa, da zaka dora ta a sikeli sai ta rinjayi duk wadancan ukun. Dalili kuwa shine, Shan giya, cin Alade ko mushe, abubuwa ne da su ka takaita a karan kan mutum ko taba wasu kalilan kusa da mai yinsu. Amma tsayar da adalci da ayar ta yi kira ko a karan kan mutum ko iyaye da mafiya kusanci, ya taba mutum, gidansa, unguwarsa, garinsa, kasarsa ya kuma tsallake addininsa ya taba kasashen Duniya da ilahirin mutanen cikinta.
To, amma sakamakon malamai ba su iya dora tarbiyar wannan Aya kamar na Shan giya ko cin mushe da Alade ba, da yawan musulmi ma ba su san ta ba, wadanda su ka santa ba su gane mahimmancinta ba ballantana su dabbaka ta cikin rayuwarsu. Amma ina rantsuwa da girman Allah babu wata Aya da ta kai mahimmancin wannan aya wajen saita rayuwa, ba ta musulmi kawai a tsakaninsu ba, hatta cudanyar mabanbantan addinai da mu’amalar kasa da kasa.
Abin mamaki hatta wadanda ba musulmi sun fahimci mahimmancin wannan aya, yadda jami’a mafi kima a yanzu a duniyar nan, wato jami’ar Harvard University da ke Amurka ta sa aka buga wannan Aya a bangon kofar shiga sashen shari’a na jami’ar. Ya kamata wannan ya zamar mana izina wajen kokarin koyawa yayanmu da ke tasowa mahimmancin wannan aya a rayuwarsu, yadda za su kaucewa fadawa irin gazawar da muka sami kanmu a ciki.
Ali Sadiƙ manazarci kuma mazaunin birnin Kano
