Obi da ’yan ƙabilanci zalla

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Wannan matsaya ta ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ga zaɓen Nijeriya na 2027 Peter Obi ta ture amfani da makircin ƙabilanci, na nuna ya yi saurin ankara cewa ‘yan kwangilar bazata a soshiyal midiya ba za su iya sama ma sa mafita a zaɓen ba. Haƙiƙa a zaɓen 2023 ya samu ƙuri’u masu yawa a tutar LEBA daga mabiya add!nin Kirista don ba mamaki yadda ita kuma APC a ka jefe ta da tsayar da dukkan ‘yan takara Musulmi. A wancan zaɓen Obi ba kawai ya tsaya da ɗan takarar mataimaki dan arewa kadai ba amma mai asali daga Larabawa wato Datti Baba Ahmad. Don haka idan ana maganar siyasar gaskiya ko Arewa, me ya kawo ƙabilanci in ba kwangilar makirci daga IP0B da sauran munafukai ‘yan bambancin addini daga Arewa ba. Shin mun manta yadda Wazirin Adamawa wanda asalinsa Basakkwace ne daga Wurno ya dau Peter Obi a mataimakin ɗan takara a PDP a 2019? Kai duk mai shigo da ƙabilanci a sha’anin siyasar nan makiri ne mai yi wa wasu miyagun mutane aiki.

A gurguje mu yi bitar mataimaka ga takara 3 da Atiku ya tsaya inda za mu ga duk mutanen na sa Igbo ne. A 2007 a jam’iyyar AC ya canki Sanata Ben Obi a matsayin mataimaki. A 2019 a PDP ya dau Peter Obi inda a 2023 a PDP ya ɗau Ifeanyi Okowa. Yanzu za mu jira mu ga wa zai dauka a ADC ga zaɓen 2027. Shin a nan waye a ka dannewa haƙƙi?

Mu dawo kan Peter Obi da tun ma bai tsaya takara ba wato bayan zaben 2023, ‘yan bazata a Arewa sun cigaba da yayata hotunansa kuma dama mun san su waye su ka zaɓe shi a 2023 OBIDIENTS. Tsakani da Allah ba wani mutum da ya cancanta ne a Arewa da mutanen nan masu cewa an danne su za su yayata hotounansa don yin takarar? Wannan ya sa a ka fahimci akwai lauje a cikin naɗi don mutanen nan ba Arewa ba ce sam-sam a gabansu. Burinsu ka iya zama biyu na farko raba Arewa ta tsakiya da Arewa ta Arewaci don farafagandar a na danne ƙananan ƙabilu sai kuma na biyu wargaza Arewa don ba wa ‘yan aware damar saukin kafa ƙasar Biyafara. ‘Yan bazata ba Hausawa ba ne sam kuma don su na rubutu da harshen Hausa ba ya nuna ruhin Hausa a jikinsu. Tarihi ya tabbatar akwai wasu ƙabilu a Arewa da su ka rasa harshe don haka su ka mannewa Hausa duk da ba su da al’adu da addinin Hausawa. In ka kalle su da kyau ma za ka gansu a fiffige 19-19.

Tabbas Peter Obi ya gano logar kuma ya barranta kansa a siyasance daga wannan kamfen na zaɓe amma a shafukan yanar gizo.

Shin wa ya ke batun ƙabila lokacin da shugaba Tinubu ya ɗau Sanata Kashim Shettima daga Borno a matsayin mataimakin ɗan takara? Duk masu caccakar kan batun addini ne kuma a dai wajen muƙamai da gwamnatin ta hau ba sauran ƙorafin addini don in ba a yi raba daidai da kowa a mukamai ba, ba wanda ya musuluntar da Nijeriya!. Shawara ta a nan kowa ya zaɓi wanda ya kwanta ma sa a rai amma a guji yin ayyukan da za su hargitsa zaman Nijeriya dunƙulalliyar ƙasa don duk mai yin haka dan gungun ‘yan aware ne masu iƙirarin ko Nzeogwu ne wanda ya yi wa Sardauna kisan giilla ya tsaya takara to shi za su zaɓa.

Haƙiƙa na sha jan hankalin jama’a kan masu ƙirƙire-ƙirƙire na sunaye da ke dangantaka da Larabci a kwangilar yaudara ta Hausa zalla. Su kan fi kowa ɓoye kansu don kasancewarsu ba lallai ‘yan Arewa ba kuma ga su Gwarawa. Kawai wani ya hau yanar gizo ba hoto ya lakabawa kansa suna ALHAWSAWI, ALHAUSAWI ko AL’ANSARI da zummar ɓoye kansa da kuma dabarar kar a gano irin imaninsa don samun sauƙin rutsawa da Hausawa. Har dai da gaske yadda mutanen nan ke nuna su na kariya ne ga Hausawa to lallai kuwa su dau sunan laƙabi da BAHAUSHE da kai tsaye shi ne HAUSAWI. Duk wanda ya bijirewa ambatar kansa da Bahaushe ya ƙirƙiro HAUWASI to tabbas ba Bahaushe ba ne kuma alamu ne na ba ma Musulmi ba ne. Aƙalla dai an san Bahaushe da addinin musulunci don haka duk wanda ke son shigar burtu don zama Bahaushen yanar gizo to sai ya ƙaƙalo HAWSAWI. Gaskiya ne akwai ‘yan karyar Hausa zalla gaulaye a kasashen Larabci amma ba sa kara Hausawi a sunayensu sai dai a kan laƙaba musu hakan in a na maganar asali.

Kwanaki wani madugun Zallawa ya yi rubutu da ƙarfafa amfani da sunayen Hausawa na ɗauri don nuna kishi kamar Tanko, Sodangi, Ciwake, Angulu da sauran su amma abin takaici shi kansa sunansa na Larabawa ne! ko kunya bai ji ba ya yi rubutun kuma har ya gama bai ayyana sauya sunansa daga na Larabawa zuwa na gargajiya ba. Gabanin nan ma ai ‘yan wannan kamfen din sun ce asalinsu ya fin a Kuraishawa ma ba ma Larabawa kawai ba. A nan duk wanda ke tafiya kan Kuraishawa ya na nuna darajarsa ta fi nan, me kuma na kakalo sunan Larabawa ya makawa kansa don batar da sawu? Ga Damuna, Rani da Tumun gero duk ba sai ya wafci ɗaya ya ƙaƙabawa kansa ba. Mutanen nan sun yi alkafura ne cikin wannan riga ta Hausawa amma ta fi karfinsu don Bagware duk dabara ba zai zama Bahaushe ba. Haba ai da mun fara magana da mutum duk wayonsa matuƙar Bagware ne za mu ramfo shi.

Ba ƙalubale ko daya da mu ka yi da ‘yan bazata su ka taɓa amsawa kama daga bayyana sunansu na gaskiya, adireshin gaskiya, addinin gaskiya zuwa hoton gaskiya. Idan mutane za su boye kansu su yi shigar burtu da wata sifar da ba ta su ba da iƙirarin kwatar haƙƙi, to duk mai nazari zai gane makirai ne masu aikin kwangilar tada fitina don cimmawa na bayan fage burinsu. A juri zuwa rafi.

Sabon ƙalubale shi ne duk mai gaskiyar cewa kishi ya ke yi na Hausa a irin wannan tafiya to ya canja laƙabi zuwa BAHAUSHE maimakon ALHAWSAWI. Mu ma ajiye batun addini da sahihancin iƙirarin hausanci, mu tsaya ga iƙirarin kishin da su ke maƙalewa a kai.

Zallawa na ta ƙoƙari su ƙara ɓoye mummunar manufarsu da ma shigewa addinin Musulunci da kudundune. Za ka ga su na iƙirarin wai su Hausawa ne kuma a cikin su akwai Musulmi, Kirista da ‘yan gargajiya. Shin wa ya taɓa ganin inda wani ya ja aya ko hadisi daga BIBLE? Wa zai ba ni wata shaida inda wani ya ja aya ko hadisi daga tsarin addinin gargajiya? Babu dukkansu ƙoƙarinsu shi ne su makale a jikin Musulunci don cutar da Hausawa. Allah wadai da wannan ɗabi’ar.

Kwangilar nan ta wargaza Arewa da ‘yan aware ke buga jaujen tabbatarwa ta hannun zallawa ba za ta taɓa cin nasara ba don ai Turawa ma masu jajayen kunne sun gwada haka su ka arce da hayaƙin tabarsu haƙarsu ba ta tadda ruwa to balle yau Baleri mai nade hannu! Allah ya jikan Dan Anache Gandi.

Haba ai mutum ba zai nesanta kansa daga iyayensa kan abun da bai sabawa muradunsa na kwangila ba. ‘Yan karyar Hausa da su ka yi dirar mikiya kan tarihin addinin musulunci cewa ba don taimakon ƙabilanci ba, da bai wanzu ba, sai su ka buge da dabarun mannewa Musulunci duk da ba su da alaƙa da addinin, wai su na ƙoƙarin nesanta kansu daga Babarsu wacce ke cewa duk zagin da za a yi ga addinin ba za ta daga ƙara ba amma sai an tabo ƙabila. To me bambancin? Ba cinya ba kafar baya.

Babarsu ta buɗe mu su ƙofar zagin Shehu Mujaddadi wanda a ta nan ba su taɓa ƙorafi ba sai kara zuga-zugi. Zagin manyan malaman Musulunci da shugabannin al’umma irin Sir Ahmadu Bello duk sun haɗa teburi ɗaya. Kai a zahiri ma kashi mai tsoka na kwangilar ba bambanci su na tare.

A nan wa waɗannan makiran za su yaudara? Ba dai irin mu ba don mu na da tocila mai batur 18 da mu kan haska ‘yan yaudarar Hausa zalla da ke son a dinga yin kisan mummuƙe da zama wutar ƙaiƙayi saɓanin yadda babarsu ke fito da kwangilar filla-filla dalla-dalla.

An yi walkiya wal-wal walai mun ga miskinai maƙiya Allah amma su na liƙewa mutan kirki a baibai don samun saukin fesa gubarsu.

KAMMALAWA

A logar mannewa Musulunci, ‘yan bazata na laƙabawa kansu sunaye irin ALHAWSAWI, ALHAUSAWI, AL’ANSARI da sauran tsari na Larabawa don hakan ya ba su damar shigewa Hausawa su yi yaudara wai kwatar ‘yanci su ke yi.

Haƙiƙa ta tabbata duk ma lokacin da a ka kai wani farmaki kan al’ummarmu a Arewa sai sun kyakyace da dariyar mugunta don haka su ke ƙauna fitina ta ki karewa a yankin don su cimmawa IPOB da MIDIBELAWA buri.

Mutanen da ke cewa sun ma fi Kuraishawa asali to ai akwai wauta ko tufka da warwara in kuma sun laƙabawa kansu sunayen Larabawa. Wa su ka rainawa wayo ne?

Duk mutanen nan ba su da alaka ta kusa ko nesa da Hausawa sai dai shigar burtu don murkushe Hausawa da yaƙi da Musulunci.

By ukarofi

Leave a Reply