
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADC ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja bisa hukuncin umarnin soke rijistarta, tana mai bayyana hukuncin a matsayin wata babbar barazana ga dimukraɗiyya da zaman lafiyar siyasa a ƙasar nan.
Haka kuma, ADC Jam’iyyar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na cire ta daga cikin jam’iyyun da za su shiga zaɓe zai iya haifar da mummunan rikicin siyasa.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne ta bakin Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi a wata takarda, inda ta ce wannan hukunci ya ƙara tabbatar da yadda jam’iyya mai mulki da gwamnati suke ƙoƙarin tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya cigaba da riƙe mulki ta kowace hanya, ko da hakan zai haifar da tauye dimukraɗiyya da jefa ƙasar cikin halin rikici.
Jam’iyyar ta jaddada cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kaɗai ikon yin rijista ko soke rijistar jam’iyyar siyasa.
Sai dai wannan hukunci ya saɓa da matsayin da INEC ta gabatar a kotu, tare da yin watsi da umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara na dakatar da cigaba da shari’ar.
Akan haka ne ADC ta sha alwashin ƙalubalantar hukuncin ta hanyoyin doka da kundin tsarin mulki, tare da kira ga mambobinta su kwantar da hankalinsu tare da jiran ƙarin umarni daga shugabancin jam’iyyar.
A yau Litinin ne babbar kotun ta umarci INEC da ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu guda huɗu kan rashin cika ƙa’idojin shiga zaɓe da dokar ƙasa da tanada.
