Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta kashe kimanin Naira biliyan 1.5 wajen gudanar da shirin ‘Auren Gata’ domin tallafawa matasa masu niyyar yin aure a jihar.
Kwamandan hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano yau.
A cewarsa, shirin zai haɗa da aurar da mutane 3,000 da suka ƙunshi amare da ango.
Ya ce gwamnatin jihar za ta bai wa kowane ango Naira dubu 100, domin ya biya sadaki, yayin da za a bai wa kowacce mace tallafin naira dubu 100 domin yin jari.
Daurawa ya kuma bayyana cewa za a horas da amaren sana’o’i domin su samu hanyoyin dogaro da kai, tare da samar musu da kayan ɗaki don fara rayuwar aure cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa ko wacce amarya za a bata setin kayan ɗaki da kayan abinci.
Kazalika ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanar da ranar da za a gudanar da ɗaurin auren.
