Bala Kefas ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule kan ayyukan cigaba

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Babban mai binciken kuɗi na gwamnatin jihar Nasarawa Mista Bala Kefas Julius yace a cikin shekaru bakwai da suka gabata gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule ta cimma ɗimbin nasarori a fannin ayyukan cigaba da ke kawo canje canje masu ma’ana ga rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya kawo yanzu.

Mista Kefas ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishin sa dake Lafia babban birnin jihar ranar Litinin na mako da ake ciki.Yace yabon gwamnan ya zama wajibi idan akayi la’akari da yadda waɗannan ɗimbin ayyukan cigaban gwamnatin waɗanda suka haɗa da gina manyan gadoji irin na zamani a Lafia da wasu ƙananan hukumomin jihar da makarantu da asibitoti da tsabtaccen ruwan sha da inganta fannin noma da hanyoyi da masana’antu da fannin tara kuɗin shiga da uwa uba inganta fannin tsaro a jihar da sauran su. Waɗanda yace a yanzu haka al’ummar jihar baki ɗaya suna alfa’ari da waɗannan ayyuka na musamman. Babban mai binciken kuɗin Mista Bala Kefas Julius ya kuma bayyana cewa bayan waɗannan ayyukan Gwamna Abdullahi Sule yana kuma tabbatar da adalci da riƙon amana a duka fannoni da suka shafi kuɗi da dukiyoyin al’umma inda yace tun zuwansa mulki bayan shekaru bakwai ba a taɓa samun gwamnatin sa da laifin al’munda’ana ko rashin gaskiya a harkokin ta ba. Inda yace wannan fannin ma gwamnan yayi rawar gani da ya cancanci yabo na musamman.

Dangane da yanayin dangantaka da ke tsakanin majalisar zartaswa ta gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ɗin da fannin dokoki Mista Kefas Bala Julius yace sannin kowa ne a yanzu haka akwai kyakkyawar dangantaka dake tsakanin ɓangarorin biyu inda ya ƙara da cewa suna aiki tare da fahimtar juna a ko yaushe kuma su kansu ‘yan majalisar dokokin na jihar suna cigaba da yaba wa gwamnan ciki ma har da ‘yan jam’iyyun adawa sakamakon aiki a zahirance da suka ganewa idanun su. Daganan sai Mista Bala Kefas Julius ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga al’ummar jihar baki ɗaya su cigaba da bai wa gwamnan cikakken goyon baya don bashi damar cigaba da samar musu da ribobin dimokuraɗiyya kamar yadda yake yi a yanzu kana ya buƙace su su cigaba da zama lafiya da junan su don a cewar sa sai da zaman lafiya gwamnati za ta iya cigaba da gudanar da waɗannan ayyukan cigaba wa al’ummar baki ɗaya.

By ukarofi