Gwamnatin Kebbi ta ayyana Talata 16 ga Yuni ranar hutun sabuwar shekarar Musulumci

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ayyana Talata 16 ga watan Yuni, ranar hutu, saboda murnar shigowar sabuwar shekarar Musulumci, 1 ga Muharram, 1448 AH.

Wata takardar sanarwa da babbar sakatariya ta ma’aikatar kula da harkokin ma’aikata da fensho da kuma horaswa, Hajiya Hafsat Ibrahim Tune, ta sanya ma hannu a Birnin Kebbi, ta ce, Gwamna Nasir Idris ne, ya amince da hutun domin marhabin da sabuwar shekarar Muslumci.

“Gwamnati na taya ɗaukacin al’ummar musulmi murnar wannan muhimmiyar ranar, kuma tana tambihi ga dukkan jama’ar Kebbi da su wanzar da addu’oin zaman lafiya da haɗin-kan al’umma da kuma samun yalwa da walwala na rayuwa da kuma tattalin arziki”,

“Kowa zai koma aiki a ranar Laraba, 17 ga Yuni”, takardan ta sanar.

By ukarofi