
Babbar Kotun Tarayya a Kaduna, ta sake ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2026.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) na tuhumar El-Rufai da laifukan amfani da ofis ba daidai ba, damfara da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin da yake gwamnan jihar.
A zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin kamar yadda rahotanni suka bayyanar, El-Rufai ya halarta tare da jami’an ICPC, DSS da kuma ’yan sanda.
Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa an fitar da wasu kuɗaɗen gwamnati domin aiwatar da ayyuka da ba a yi ba ko kuma aka gudanar da su ba bisa ƙa’ida ba.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa ba shi da hannu a wani laifi.
Tun da farko kotun ta ba shi beli kan kuɗi Naira miliyan 200 tare da wasu sharuɗɗa, yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar.
Alƙalin kotun ya ɗage shari’ar ne bayan wasu mutane biyu da ake tuhuma tare da El-Rufai sun kasa halartar zaman.
