
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADC ta sanar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, shi ne wanda zai yi wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar mataimaki yayin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke cigaba da kusantowa.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai domin ƙarfafa matsayinsu a fagen siyasar Nijeriya musamman bisa la’akari da yadda fagen ke cigaba da ɗaukar ɗumi.
Ana kallon tikitin Atiku da Amaechi a matsayin wani gagarumin yunƙuri na samar da zaɓin shugabanci daban ga ‘yan Nijeriya ganin yadda salon ‘yan adawar ke ɗaukar hankalin al’umma.
A cewar rahotanni, bayan shawarwari da tattaunawa tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, Amaechi ya amince da zama abokin takarar Atiku domin cimma manufofin jam’iyyar da kuma fuskantar babban zaɓen.
