
Daga ABUBAKAR a BOLARI Gombe
Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta nuna damuwa kan tsananin cunkoson da ake fama da shi a Gidan Gyaran Hali na Gombe, inda ta bayyana cewa gidan yarin da aka gina domin ɗaukar fursunoni 390 kacal, a halin yanzu yake ɗauke da sama da fursunoni 1,000.
NBA ta bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ta kai gidan gyaran halin a matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin Makon Lauyoyi na shekarar 2026, inda ta kuma samu nasarar tabbatar da sakin fursunoni tara.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ziyarar, Shugaban NBA na reshen Gombe, Barista Alhassan Mu’azu, ya ce manufar ziyarar ita ce tattaunawa da fursunoni da jami’an gidan gyaran hali domin fahimtar ƙalubalen da suke fuskanta tare da nemo hanyoyin inganta gudanar da adalci.
Ya bayyana cewa, gidajen gyaran hali na daga cikin muhimman masu ruwa da tsaki a fannin shari’a, don haka akwai buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin dukkan hukumomin da abin ya shafa.
Ya ce, “Mun zo ne domin mu nuna musu cewa muna tare da su, mu saurari matsalolinsu, sannan mu ga irin gudunmawar da za mu bayar wajen magance wasu daga cikin ƙalubalen da ke addabar wannan cibiya.”
Barista Mu’azu ya kuma bayyana cewa, ta hannun ƙungiyar, an samu nasarar sakin fursunoni tara daga sassa daban-daban na jihar.
Ya ce, “A matsayin wani ɓangare na bikin Makon Lauyoyi na 2026, NBA ta yi nasarar tabbatar da sakin fursunoni tara.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun fito ne daga ƙananan hukumomin Nafada da Billiri, yayin da sauran kuma suka fito daga Gombe.”
Sai dai ya nuna damuwa matuƙa kan yadda gidan gyaran halin ya cika da fursunoni fiye da ƙarfinsa.
“A cewar bayanan da aka gabatar mana, an gina wannan gida ne domin ɗaukar mutum 390. Amma a yau yana ɗauke da sama da fursunoni 1,000. Wannan ya nuna irin nauyin da ke kan jami’an gyaran hali da kuma buƙatar samun ɗorewar tallafi daga masu ruwa da tsaki,” in ji shi.
Shi ma da yake jawabi, Mataimakin Kwanturolan Hukumar Gyaran Hali mai kula da gidan, Victor Odafe, ya yaba wa NBA bisa ci gaba da haɗin gwiwa da tallafin da take bai wa Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya.
Ya yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara tallafa wa gidajen gyaran hali domin su samu damar fuskantar ƙalubalen da ke ƙaruwa a kullum.
Ya ce, “Muna godiya da irin tallafin da muke samu lokaci zuwa lokaci, musamman a lokutan bukukuwa. Amma har yanzu muna buƙatar ƙarin taimako.
Ya dace a ci gaba da bai wa gidajen gyaran hali kulawa da goyon bayan da ake bai wa sauran fannoni.”
A yayin ziyarar, ƙungiyar NBA ta kuma raba kayan tallafi ga fursunonin a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai da ta gudanar a bikin Makon Lauyoyi na shekarar 2026.

