Pakistan ta sanar da shirin tsagaita wutar yaƙin Amurka da Iran yayin da Trump ya tabbatar da yarjejeniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Akwai yiwuwar yiwuwar a dakatar da kai hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya bayan ƙasar Pakistan ta sanar da cewa Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta da kuma wata yarjejeniyar zaman lafiya da ke da nufin kawo ƙarshen rikicinsu, wanda ya kawo cikas ga kasuwannin makamashi a duniya.

Fraministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya ce an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, yayinda ake sa ran gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Yuni a ƙasar Switzerland.

A nasa ɓangaren, Shugaba Donald Trump na Amurka ya tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, yana mai sanar da kawo ƙarshen rufe mashigin ruwa na Hormuz da ke ƙarƙashin ikon Iran da Oman.

Ɓangarorin biyu sun amince da dakatar da duk wani aikin soji nan take kuma na dindindin a dukkan wuraren da rikicin ya shafa, ciki har da Lebanon da wasu sassan yankin Gulf.

A cewar Trump, an cimma yarjejeniyar ne bayan tattaunawa mai zurfi, inda Pakistan ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani, matakin da ƙasashe da dama na duniya, ciki har da Ƙatar da Birtaniya da Rasha, suka yi maraba da wannan ci-gaba.

Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen Ƙatar, Sheikh Mohammad bin Abdurrahman Al Thani, ya ce ƙasarsa tana maraba da yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka da Iran suka cimma wanda ake fatan ya kawo gagarumar ci-gaba a harkokin Gabas ta Tsakiya.

By Babaji

Leave a Reply