Alhinin rasuwar Janar Rabe ta sa Tinubu fasa sulhu da ‘yan bindiga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar tsohon jami’in soja, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu bayan ya shiga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina, inda Shugaban Ƙasar ya nuna cewa, babu sauran sulhu tsakaninsu da ‘yan bindiga.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar ranar Asabar, Tinubu ya ce rasuwar Janar Abubakar abin takaici ne ga ƙasa baki ɗaya, musamman ganin irin gudunmawar da ya bayar wajen kare Nijeriya a lokacin da yake aikin soja.

Rahotanni sun nuna cewa Janar Abubakar yana kan hanyarsa ta komawa garinsu ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka tare shi da yin garkuwa da shi.

Shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman matarsa wadda har yanzu take hannun masu garkuwa da mutanen.

Haka kuma ya jajanta wa gwamnatin Jihar Katsina da rundunar sojojin Najeriya bisa wannan babban rashi.

Tinubu ya jaddada cewa duk da wannan lamari mai raɗaɗi, gwamnatin tarayya ba za ta amince da buƙatar masu garkuwa da mutane ko ’yan ta’adda ta sakin waɗanda jami’an tsaro ke tsare da su ba.

Ya tunatar da ’yan Nijeriya kalaman da ya yi a ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, inda ya gargadi ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyinsu da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci ƙarfin ikon ƙasar.

“Masu garkuwa da mutane, ’yan bindiga da masu ɗaukar nauyin ta’addanci su sani cewa damar miƙa wuya ba za ta kasance a buɗe har abada ba. Ba za a nuna jin ƙai ga waɗanda ke cinikin jinin ’yan Najeriya ba,” in ji shugaban ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa dole ne ’yan Nijeriya su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro, yana mai cewa nan gaba kaɗan za a kawo ƙarshen ta’addanci da hare-haren ’yan bindiga a ƙasar.

A cewarsa, rasuwar Janar Rabe Abubakar ya kamata ta zama wani babban darasi a yaƙin da Najeriya ke yi da ta’addanci, inda ya ce bai kamata gwamnati ta shiga tattaunawa ko yin sulhu da masu aikata irin waɗannan laifuka ba.

“Waɗannan su ne manyan maƙiyan ƙasarmu, kuma dole ne a ci gaba da fuskantarsu da dukkan ƙarfin gwamnati har sai an kawo ƙarshen ayyukansu,” in ji Tinubu.

Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar ya taɓa zama kakakin ma’aikatar tsaro ta Najeriya, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin da suka gabata.

By ukarofi

Leave a Reply