Yadda shirin ‘Kannywood Abba Care’ ya buɗe ƙofar kula da lafiyar masu finafinan Hausa 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A tsawon shekaru, ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da suka daɗe suna addabar masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood shine yayata matsalar kula da lafiyar masu ruwa da tsaki a cikinta. Duk da irin gudunmawar da masana’antar ke bayarwa wajen nishaɗantarwa da bunƙasa al’adu, an sha ganin fitattun jarumai, mawaƙa da sauran masu sana’o’in da suke da alaƙa da sana’ar suna fuskantar matsalolin rashin lafiya ba tare da samun isasshen tallafi ba.

Sai dai a wani sabon yanayi da ya jawo farin ciki a tsakanin zukatan masu harkar, an bayyana wani shiri da ake ganin zai kawo sauyi a fannin kula da lafiyar ‘yan Kannywood, bayan wata ganawa mai muhimmanci da ta haɗa shugabannin masana’antar, Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da kuma Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano.

Bayanan da suka fito daga shugabanin ƙungiyar MOPPAN sun nuna cewa, an gudanar da wannan muhimmin zama ne a ranar 4 ga watan Yunin 2026 da misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, inda aka tattauna hanyoyin da za a tallafa wa mambobin masana’antar da suka jima suna fama da matsalolin lafiya.

Rahoton ya nuna cewa wannan mataki ya samu ne bayan Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Abba Almustapha, ya kai koken halin da wasu daga cikin masu harkar Kannywood ke ciki ga Babbar Sakatariyar Hukumar KSCHMA, Hajiya Rahina. A cewar bayanan, ya nemi a duba yiwuwar samar da wani tsari da zai ba ‘yan masana’antar damar samun kulawar lafiya cikin sauƙi.

An bayyana cewa, wannan yunƙuri ya samu karɓuwa daga hukumar, lamarin da ya haifar da fara ɗaukar matakan tallafa wa wasu daga cikin mambobin Kannywood da ke fama da matsalolin rashin lafiya.

A matakin farko na wannan shiri, an bayyana cewa, an fara kula da wasu daga cikin fitattun mambobin masana’antar da suka haɗa da Aminu Mahiru da Haruna Titibiri da Ladidi Fagge da Abubakar Hunter da Mustapha Musty da Zainab Golden tare da Zakiyya Ibrahim.

Shugabannin masana’antar sun bayyana wannan mataki a matsayin wata alama ta nuna damuwa da kula da jin daɗin masu harkar fina-finai, musamman waɗanda suka shafe shekaru suna hidima ga masana’antar.

Baya ga waɗanda aka fara tallafawa, bayanan sun nuna cewa, an bai wa mahalarta taron fom domin cike bayanan rajista tare da zaɓar asibitin da suke son samun kulawa a cikinsa idan buƙatar hakan ta taso.

A cewar masu shirya shirin, manufar ita ce a bai wa duk wani ɗan Kannywood da ke da buƙata damar cin gajiyar tsarin, yayin da za a sanar da hanyoyin samun fom da sauran ƙa’idojin shiga cikin shirin nan gaba kaɗan.

An kuma sanya wa wannan tsari suna “Kannywood Abba Health Care”, wanda ake sa ran zai zama wata muhimmiyar hanya ta bunƙasa walwala da jin daɗin masu harkar fina-finai a jihar.

Bayan kaddamar da wannan yunƙuri, shugabannin masana’antar sun bayyana aniyarsu ta shirya wani gangami domin nuna godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa irin tallafin da ake ganin gwamnatinsa ta bayar wajen tabbatar da ganin an samu wannan dama ga mambobin Kannywood.

Wakilan ƙungiyoyi daban-daban da suka haɗa da MOPPAN da Arewa da Elders da Actors da kuma KAFIGAN ne suka halarci taron da ya haifar da wannan matsaya.

A wani ci gaba da ya biyo bayan wannan nasara, an fitar da wasiƙar naɗa Alhaji Shehu Hassan Kano a matsayin Shugaban Kwamitin Kannywood Abba Care.

Wasiƙar, wadda aka sanya wa hannu daga Sakataren Kwamitin, Salisu Mohammed, ta bayyana cewa an yanke shawarar kafa kwamitin ne domin kula da aiwatar da shirin, haɗa kai da masu ruwa da tsaki, wayar da kai, tattara masu rajista da kuma kasancewa gada tsakanin gwamnati da masana’antar.

A cikin wasiƙar, an bayyana cewa an zaɓi Shehu Hassan Kano ne saboda halayen jagoranci, ƙwarewa, amana da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban masana’antar Kannywood.

Nadin nasa ya fara aiki daga ranar 8 ga watan Yunin 2026.

Baya ga shugaban kwamitin, an kuma sanar da wasu mambobi da za su taimaka wajen tafiyar da ayyukan shirin.

Kwamitin ya ƙunshi Salisu Mohammed a matsayin sakatare, yayin da Hadiza Maikano da Idris Shuaibu Lilisco da Auwal Marshal da Isma’il Khalil Ja’en da Auwal Anwar da Kabiru Maikaba da Aminu Acid da Dr. Mohammed I. Gumel za su kasance mambobi.

Abin da ya fi ɗaukar hankali a wannan lamari shi ne, yadda batun kula da lafiyar masu harkar Kannywood ya samu shiga cikin wani tsari na hukuma wanda zai bai wa mambobin masana’antar damar samun kulawar lafiya cikin sauƙi.

Ko da yake lokaci ne kawai zai nuna girman tasirin wannan shiri, amma bayanan da suka fito daga tarurrukan da aka gudanar sun nuna cewa an ɗauki matakin ne da nufin inganta walwala da jin daɗin masu sana’ar fina-finan Hausa, tare da samar musu da wata kafa da za ta taimaka wajen samun kulawar lafiya a lokacin da buƙata ta taso.

A idon masu lura da al’amuran masana’antar, wannan na daga cikin matakan da suka fi jan hankali da suka shafi walwala da kariyar zamantakewar masu harkar Kannywood a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ake kallon shirin a matsayin wani sabon shafi a tarihin masana’antar.

By ukarofi

Leave a Reply