Daga ABDULYASSAR AMINU ABUBAKAR
A duk lokacin da aka ce an tashi ba da wani misali ko kuma kwatance a kan Kannywood, to fa babu wata masana’anta da ake hada kwatancen na su illa Bollywood ko Tollywood. Abin zai iya yin ciwo a ranka ace kana kallon kai kana ta ƙoƙari domin girmamar da kanka amma wasu gungu na yi maka kallon ba ka ma da niyya, ko ba ka ma fara ba.
In dai mutum na bibiyar al’amuran fina-finan Indiya musamman ma na kudanci, watau Tollywood, lalle ne zai riƙa ganin irin fashin bakin da Aliyu Wazzyyr ke yi. Kuma yana matuƙar ƙoƙari gaskiya. Dazun aka yi ta tagging dina kan wani fashin baki da ya yi a kan yadda fina-finan Indiya ake shafe tsawon kwanaki sittin ga manyan kamfanunuwa, arba’in ga kanana yayin da aka ce an zo ɗaukarsu. Da kuma adadin Crews da kowanne kamfani ke ɗauka, daga manyan har ƙnanan, shi ma da kan sa har yana tambaya, “Wai ya ya abin yake a Kannywood?”
Ga amsar:
Mukan ɗauki aƙalla wata guda muna ɗaukar fim ko sama da haka yayin da muke aiki, kuma hakan ga babban ‘production’ ne. Kamar dai yadda ya ce suma hakan na faruwa ne a manyan Production a Bollywood.
Muna aiki da ‘Crews’ sama da ashirin da biyar, na kowanne fanni. Kamar yadda ya ce a Bollywood, babban kamfani suna aiki da aƙalla mutane talatin ko sama, ƙarami kuma daga ashirin zuwa sha biyar.
Watau akwai wani abu da nake son mutanenmu su fahimta game da Kannywood. Kannywood ɗin jiya, ba fa ita ce a yau ba, kullum da neman ilimin fim ɗin muke da duk wani abu da ya danganci fim.
Ko da kuka ga kusan kodayaushe muna kira da a yi gyara a cikin masana’antar, gyaran da muke magana a yi daban ne da wanda kuke tunani. Wanda kuke yi a bisa hasashen ku ne kawai na masu kallo, yayin da mu wanda muke yi ba haka ba ne.
Babban abin da ke yawan bani mamaki shi ne yadda a duk lokacin da aka tashi kushe Kannywood, cewa ake babu kayan aiki, ba a iya ba ace za a yi.
Mene ne kayan aikin da kuke magana a kai? Cameras ne. Kuma su ma Bollywood da sauran Wood ba su wuce waɗannan cameras din ba: Red, Red Dragon, Red Effect, Arri Aleɗa, Sony, Black Magic 6K ko 12K.
Zuwa yanzu ma Kannywood na amfani da irin waɗannan cameras: Red, Sony Fɗ3, Black Magic 6K da 12K. Ka ga dai kenan ana tsaka da isa ga abin da ake so a je. Akwai wani abu da kuke kallo da har yake sanya ku ganin Kannywood ba ta da kayan aiki. Mafi yawancin sauran Wood’s ayyukan Studio suke yi, ma’ana dai ayyukan da Editing ke cin ƙarfi bayan ɗaukarsu.
Mafi yawancin ayyukansu suna yi ne da Green Screen, Blue Screen, har ma wani lokacin White Screen, watau CGI (Computer Generated Imagery) ke ɗaukar kaso mai yawa na abin da kuke gani a ƙarshe.
Amma a Kannywood, mafi yawanci ana aiki ne da real location shooting. Watau dai komai na gaske ne:
1. Gine-gine
2. Motoci
3. Mutane
Kai hatta dabobi idan kuka gan su a fim ɗin Hausa, ba ƙirƙirar su aka yi ba na zahiri ne. Ka ga don sun kai adadin waɗancan kwanaki ba za a ce kwarewa ce kawai ba, sai dai mu ce yanayin aiki ne daban. CGI na rage lokaci a wasu industries, amma kuma yana buƙatar babban budget.
Kamar irin su:
1. Heavy post-production team
2. Advanced VFɗ pipeline, wanda shi ma ba a ko’ina ake da shi yin sa ba.
Ba za mu daina faɗi ba, ‘yan kasuwarku su riƙa shigowa cikin masana’antar suna sanya hannun jarinsu, duk abin da kuke muradi za ku gani, har ma da wanda ba ku yi tunani ba.
Sai kuma wani ɗan kira da zan yi gare mu: Zamanka me bashin baki ko sharhi kan fina-finai ba aibi ba ne, amma ka da ka riƙa taɓo ababen da gundarin ilimin fim ne saboda lamarin na zama wani kala daban.
Abdulyassar (The Beacon of Light) ya wallafa ne a shafinsa na Facebook
