Kada a yi wannan fim don samar da zaman lafiya ga juna

Spread the love

Daga ABDULYASSAR AMINU ABUBAKAR

Duk lokacin da aka ce an rasa kusanceceniyar alaƙa da gundarin fahimta a koma wanne bigire ne, lallai babu wata hanya da za a fahimci juna har ma a shirya wasu abubuwan cigaba ko kuma da za a samu har ’yan baya ma su mora.

Bari na yanke zancen. ɗazun kenan na ga wannan fasta da kamfanin Sultan Film Factory za su ɗauka (Aure Goma). Ban sani ba sun fara ‘shooting’ ko kuwa ba su fara ba, Allah shine mafi sani. To, amma Ina da shawara. Ga yadda na ga ya yi ‘posting’, alamu ya nuna zai yi wani labari ne da zai taɓo rayuwar gidan aure ko na ce ma’aurata. To, amma me hakan zai haifar ne?

Kwana-kwanan nan (Furodusa) Abdul Amart ya ɗauko wani labari (Kaddara) da ke zayyana rayuwar aure da matsalolin gidan auren kansa. To, ka ga kenan, babu buƙatar kawo labari makamancinsa ko mai irin zubinsa, domin ba zai taɓa samun magoya baya ba. Idan ko har aka samu, to zan iya cewa na ɗan lokaci ne, domin ko da marubucin ya so kauce abin da aka yi a fim ɗin Kaddara, to lallai zuwa gaba sai ya dawo. Madadin haka, gara Sultan ya ɗauki marubuta su zage su rubuta masa wani rantsattsen labarin. Na san kuma za ka iya zuba ko da nawa ne, domin kasuwar fim ba ta taɓa ba ka tsoro ba.

Amma idan har ka yi wannan fim, kamar yadda ka fara bayar da ‘pitching’ na ‘story’, tom abin da zai fara zuwa ran mutane da dama shine, da biyu, ko don a yi rikici ka ɗauko wannan aiki. Dalilina a nan shine, lokacin da Abubakar Bashir Maishadda ke tsaka da Gidan Sarauta, a daidai lokacin ka yi ‘post’ kan cewar za ka yi wani fim A Gidan Sarauta. Idan dai ban mance ba, haka ne sunan film ɗin.

Ina fatan kowanne ɓangare za su yi adalci ba tare da sun kalli rubutuna a matsayin wata hanya ta shirya rikici ko dalilin da zai harzuƙa su. Ba ga yaran Sultan ba, ko kuma yaran Producer Abdul Amart. Na yi wannan rubutu ne don fargar da duk wani ‘Producer’ da ke da tunanin ganin ‘title’ ko wani nau’i na labari na tafiya ya ce shi ma bari ya yi irinsa ba tare da tunanin me hakan kan janyo a gaba ko ma a nan kusa ba.

Malam Abdulyassar (The Beacon of Light) marubuci ne kuma manazarci a Kannywood

By ukarofi