Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Jami’ar hulɗa ta UN Women ga gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Fatima Muhammad Paga, ta yi kira ga ‘yan majalisar tarayya da su amince da ƙudirin kujeru na musamman ga mata, tana mai bayyana shi a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa wakilcin mata a harkokin siyasar Najeriya.
Paga ta ce amincewa da ƙudirin zai buɗe ƙarin damammaki ga mata domin su taka rawa sosai wajen tsara manufofi da yanke shawarar da suka shafi ci gaban ƙasa.
A cewarta, duk da irin gudunmawar da mata ke bayarwa wajen bunƙasa al’umma, har yanzu ba su da isasshen wakilci a manyan muƙaman shugabanci da na siyasa a ƙasar.
Ta jaddada cewa samar da kujeru na musamman ga mata zai taimaka wajen gina shugabanci mai cike da wakilci da adalci, tare da bai wa mata damar bayar da gudunmawarsu yadda ya kamata wajen ci gaban Najeriya.
Haka kuma, ta yi kira ga ‘yan majalisa, jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su mara wa shirye-shiryen da ke inganta shigar mata cikin harkokin shugabanci baya.
Paga ta bayyana fatan cewa idan aka amince da ƙudirin, hakan zai ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya tare da tabbatar da tsarin shugabanci da ya fi wakiltar kowane ɓangare na al’umma.
