Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Wakilai ya bayyana cewa ya samu nasarar ƙwato kusan Naira biliyan 522 na Harajin ƙarin Kima, wato VAT, da ba a miƙa wa Gwamnatin Tarayya ba daga hannun Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Kwamitin ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga binciken da yake ci gaba da gudanarwa kan zubewar kuɗaɗen shiga da kuma kuɗaɗen da ya kamata a biya Gwamnatin Tarayya amma ba a biya ba.
A cewar kwamitin, wannan kuɗi da aka kwato na daga cikin sakamakon wani cikakken bincike da aka ƙaddamar bayan Majalisar Wakilai ta amince da wani ƙudiri da ya nemi a binciki yadda ake samun asarar kuɗaɗen shiga ta hanyar tsarin biyan kuɗi na Remita da kuma rashin bin ƙa’idojin gudanar da aiki yadda ya kamata.
Shugaban kwamitin, Hon. Bamidele Salam, ya bayyana a ƙarshen mako cewa binciken ya haifar da ƙwato kuɗaɗe masu yawa tare da gano wasu basussukan da har yanzu ake bin wasu hukumomi domin su mayar da su cikin baitul malin gwamnati.
Kwamitin ya ce bincikensa ya gano cewa Babban Bankin Nijeriya ya gaza tura Harajin ƙarin Kima (VAT) da ya kai Naira biliyan 521.8, wanda ya kasance harajin da ya kamata a biya daga kuɗaɗen hidimomin da aka samu ta hanyar mu’amalolin Remita.
Sakamakon haka, kwamitin ya umarci Babban Bankin Nijeriya da ya gaggauta mayar da kuɗin cikin Asusun Baitul Malin Gwamnatin Tarayya tare da gabatar da shaidar cewa ya bi umarnin.
Rahoton binciken kwamitin ya nuna cewa kuɗaɗen harajin da ba a tura ba sun taru ne tsakanin watan Nuwamban 2018 zuwa watan Afrilun 2024.
Sai dai a wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 7 ga Mayu, 2026, Babban Bankin Nijeriya ya sanar da kwamitin cewa ya riga ya bi umarnin da aka ba shi tare da mayar da kuɗaɗen da ake magana a kansu.
Lamarin ya ƙara nuna yadda binciken da Majalisar Wakilai ke yi kan kuɗaɗen shiga da tsarin tattara haraji ke gano kura-kurai da giɓin kuɗaɗe da ke hana gwamnati samun cikakken kuɗaɗen shigarta.
