Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fannin samar da wutar lantarki a Nijeriya na fuskantar sabon ƙalubale bayan da bashin da kamfanonin samar da wuta (GenCos) ke bi ya haura zuwa Naira tiriliyan bakwai, yayin da kamfanonin suka yi watsi da tsarin da Gwamnatin Tarayya ta gabatar na sasanta bashin.
Babbar Sakatariya kuma Babbar Daraktar ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (APGC), Dakta Joy Ogaji, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin ƙaddamar da taron horas da shugabannin fannin wutar lantarki na Nijeriya na shekarar 2026.
A cewarta, nauyin bashin da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bi na ci gaba da ƙaruwa duk da ƙoƙarin gwamnati na warware matsalolin basussukan da suka dabaibaye Masana’antar Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NESI).
Tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta amince da wani shiri na biyan bashin naira tiriliyan 3.3 domin warware tsofaffin basussukan da suka taru tsakanin shekarar 2015 zuwa farkon shekarar 2025. Shirin ya tanadi biyan bashin ne ta hanyar takardun alƙawarin biyan kuɗi na tsawon shekaru 10 da kuma kuɗaɗen da za a samu daga takardar bashi ta naira biliyan 501.02 da Kamfanin Kasuwancin Wutar Lantarki na Nijeriya (NBET) ya fitar.
An tsara wannan takardar bashi ne a matsayin matakin farko na wani babban shiri da zai rage gibin kuɗaɗen kasuwar wutar lantarki tare da dawo da amincewar masu zuba jari a fannin.
Sai dai aiwatar da shirin ya tsaya cik sakamakon saɓanin da ya taso kan ainihin adadin bashin da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarkin.
Dakta Ogaji ta bayyana cewa adadin bashin da gwamnati ta tabbatar da shi na tiriliyan 3.3 ya ƙaru zuwa tiriliyan 3.8 kafin naɗin Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Wutar Lantarki, Rilwan Lanre Babalola, sannan daga bisani ya kusan kaiwa tiriliyan 7 sakamakon ci gaba da taruwar takardun kuɗaɗen da ba a biya ba.
Ta jaddada cewa har zuwa yanzu kamfanonin samar da wutar lantarki ba su karɓi wani sabon biyan kuɗi ba duk da alƙawuran da gwamnati ke yi.
“Har zuwa yau ba mu samu ko sisi ba. Kuma ba mu amince da tsarin biyan bashin tiriliyan 3.3 da gwamnati ta gabatar ba,” inji ta.
Ta kuma bayyana cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta fitar da cikakken kuɗin naira biliyan 500 da aka tara ta kasuwar takardun bashi a watan Disamba domin biyan wani ɓangare na basussukan ba.
Kazalika, ta ce kamfanonin samar da wutar lantarki sun yi watsi da shawarar da ke neman su yafe rabin bashin da ake binsu, tana mai cewa har masu samar da iskar gas ma sun ƙi amincewa da wannan tsari.
A cewarta, ƙoƙarin da aka yi na shawo kan masu samar da gas su amince da rage musu kashi 50 cikin ɗari na bashin da ake binsu bai yi nasara ba.
“Lokacin da muka sanar da masu samar da gas cewa gwamnati ta yanke shawarar cire rabin bashin, sai suka ce ba za su amince ba kuma suka gaya mana cewa mu ne ke da matsalar,” inji ta.
Ogaji ta yi gargaɗin cewa ci gaba da ƙaruwa irin wannan bashin na barazana ga samar da wutar lantarki da kuma daidaiton fannin gaba ɗaya, domin kamfanonin na fama da matsin tattalin arziki wajen gudanar da ayyukansu.
Ta yi kira ga sabon Ministan Wutar Lantarki, Joseph Olasunkanmi Tegbe, da ya nuna ƙwazo da ƙarfin siyasa ta hanyar ayyana dokar ta-baci a fannin tare da ɗaukar matakan gaggawa da za su dakatar da ƙarin taruwar basussuka.
Ta ce, warware tsofaffin basussuka kaɗai bai isa ba, sai an samar da tsarin biyan kuɗi mai ɗorewa domin hana sake komawa cikin irin wannan matsala nan gaba.
“Abu na farko da ya kamata ya mayar da hankali a kai shi ne dakatar da ci gaba da ƙaruwa na bashin tare da magance wanda ya riga ya taru,” inji ta.
Masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki sun sha yin gargadin cewa idan ba a warware matsalar bashin ba, masu zuba jari za su ƙara ja da baya daga fannin, lamarin da zai ƙara ta’azzara matsalar ƙarancin wutar lantarki da Nijeriya ke fama da ita.
