Gwamnatin Zamfara ta jinjina wa NAHCON kan aikin hajjin 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta samu saƙon yabo daga Gwamnatin Jihar Zamfara bisa ƙoƙarinta wajen sauke nauyin aikin Hajjin 2026 cikin kyakkyawan tsari.

A wasiƙar, wanda ke ɗauke da sanya hannun Sarkin Anka kuma Amirul Hajji na jihar, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, an yaba wa NAHCON bisa hoɓɓasa da ta yi wajen sauke nauyin walwalar mahajjatan bana.

A cewarta, “Salon da ya shafi shirye-shiryen ciyarwa da masauki a Madinah da Mina sun nuna samun gagarumar ci-gaba a walwalar alhazan Jihar Zamfara.”

Kwamitin Amirul Hajjin na Zamfara ya jinina wa Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf bisa kyawun tsare-tsaren da ya ƙaddamar da kulawa da walwalar mahajjata a lokacin ibadar da kuma jigilarsu.

A ƙarshe, kwamitin ya yaba wa hukumar gudanarwar NAHCON da ma’aikatanta bisa sadaukarwarsu na hidimta wa al’ummar Musulmi, yana mai addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi da kuma ƙara wa hukumar albarka yayin gudanar da harkokinta.

By Babaji

Leave a Reply