Manyan jami’an tsaro sun kai ziyarar ta’aziyar Janar Rabe a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Joɓe ya amshi tawaga ta musamman daga hedikwatar tsaro ta ƙasa domin jajantawa gwamnatin Jihar Katsina bisa rasuwar Manjo Janar Rabe Abdullahi mai ritaya.

Tawagar ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar IM Abdullahi (Chief Admin Officer Defence Headquarters) ta ƙunshi Manjo Janar WB Idris (Theater Comd) R. Admiral AH Haruna, Manjo Janar BP Koughna, Birgediya Janaral IM Ibrahim, Birgediya Janar SK Usman (rtd) AUM SI Kaita (rtd) Manjo Janar MS Bindawa (rtd) da AUM AY Abdullahi.

A jawabin sa, shugaban tawagar Manjo Janar IM Abdullahi yace sun ziyarci jihar Katsina ne domin jajantawa gwamnati da alummar jihar bisa rasuwar Manjo Janar Rabe Abdullahi wanda ya rasa rayuwar sa a hannun ‘yan bindiga.

Manjo Janar IM Abdullahi ya bada tabbacin hedikwatar ta rundunar tsaron ƙasa za ta zaƙulo waɗanda ke da alhaki wajen kisan Manjo Janaral Rabe Abdullahi mai ritaya.

Da yake jawabi a madadin gwamnatin Jihar Katsina, mataimakin gwamnan Malam Faruk Lawal yayi maraba da ziyarar rundunar tsaron ya Kuma bada tabbacin gwamnatin Jihar Katsina wajen haɗa hannu da hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin daya dace wajen hukunta masu hannu a kisan Manjo Janaral Rabe Abdullahi Mai ritaya.

Mal Faruk Lawal ya bayyana cewa gwamnatin Jihar na bakin ƙoƙarin ta wajen kare rayuwa da dukiyoyin al’umma dan haka akwai buƙatar ƙarin jajircewa daga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace ga ɓatagari a faɗin jihar ta Katsina dama ƙasa baki ɗaya.

A lokacin ziyarar an gudanar da shiru na minti ɗaya da nufin nuna alhinin rasuwar Marigayi Rabe Abdullahi mai ritaya.

By ukarofi

Leave a Reply