
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alhazan Jihar Legas guda 1,600 da suka je aikin Hajjin 2026 ne suka koma gida lafiya daga Saudiyya bayan kammala ibadar.
Dawowar tawagar ƙarshe na mahajjata 187 a ranar Asabar ya nuna kammala aikin hajjin na 2026.
Da yake ganawa da manema labarai a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Amirul Hajji kuma Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Legas, Ibrahim Layode ya ce gudanar da ibadar babbar nasar ce ga Jihar Legas.
Ya kuma alaƙanta nasarar da gudanar da ayyukan mahajjatan bisa kyakkyawan tsari a ƙasa Mai Tsarki, yana mai cewa Jihar ta ɗauki matakin shirye-shiryen da suka dace ta hanyar damawa da dukkan masu ruwa da tsaki acikin al’amarin.
Ya kuma bayyana matakan da suka bi wajen cika sharuɗɗa da ƙa’idojin da Saudi ta gindaya musamman don ganin ta kammala dukkan abin da ake buƙata gabanin cikar wa’adin da aka bayar.
Kazalika, Kwamishinan ya yaba wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas da Maitaimakinsa, Dakta Kadiri Hamzat bisa gudunmawarsu ga alhazan, yana mai cewa tallafin da suka bayar ya taimaka wajen gudanar da aikin cikin nasara.
A nasa jawabin, Mai taimaka wa gwamnan Legas akan Harkokin Addinin Musulunci kuma Shugaban Ƙwarya-ƙwaryan kwamitin Hajji, Dakta Abdullahi Jebe ya ce jihar ta shirya tsarin tabbatar da dabarun aiwatar da harkokin hajji, yana mai bayyana hakan a matsayin salon da ake bi wajen yin nasara a shekarun da suka gabata.
