Gwamnatin Tarayya fara shari’ar mutum 400 da ake zargi da ta’addanci a kotun Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutane 400 da ake zargin su da hannu a ayyukan ta’addanci.

An gudanar da shari’o’in ne a ɗakin kotuna da Babbar Kotun da ke Abuja.

Tawagar masu gabatar da shari’ar ta ƙunshi Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi a matsayin shugaba da kuma Daraktan Harkokin Shari’o’in Gwamnatin Tarayya, Rotimi Oyedepo (SAN).

Ana tuhumar mutane 400 ne da hannu a laifukan da aka alaƙanta da ta’addanci, taimakawa da ɗaukar nauyin ayyukan tayar da ƙayar baya.

Babban Mai Shari’ar kotun, John Tsoho, ta tawagar alƙalai ne suka jagoranci shari’o’in. Wasu daga cikin alƙalan sun haɗa da Binta Nyako, Emeka Nwite, Musa Liman, James Omotosho, Obiora Egwuatu, Ekerete Akpan, da dai sauran su.

Gwamnatin Tarayyar ta ɗauki matakin ne don kawo ƙarshen yawan jinkirin da ake samu wajen yin hukunci akan shari’o’in da suak shafi ta’addanc a Nijeriya, inda ake yin su yanzu a Abuja, a madadin kotun sojoji da ke Kainji a Jihar Neja.

Aƙalla kimanin mutane 58 ne aka ware don yi musu shari’a a gaban Mai Shari’a Nwite.

Daga cikinsu akwai Abba Bukar, Abba Manye, Gujja Mala Bukar, Brem Gonimi, Isa Mohammed, Lawali Dashiri Danke, Yau Tukur (Mai-Auduga), Bello Liman, aka Alhaji Bell Doctor, da sauransu.

Mutane 500 da ake zargi da ta’addanci ne aka gurfanar daga ranakun 7 da 10 ga Afrilu a babbar kotun.

By Babaji

Leave a Reply