Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da shirin horar da malamai 1,000 a faɗin jihar don inganta Ilimi a faɗin makarantun Jihar.
Kwamishinan Ilimi, kimiyya da fasaha, Malam Abdulmalik Gajam, ya bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai a Gusau.
A cewar kwamishinan, an tsara shirin ne don haɓaka ƙwarewar malamai da inganta tsarin koyo da koyarwa a makarantun gwamnati.
“Manufar wannan horon ita ce gina ƙarfin malamanmu da kuma haɓaka ingancin koyarwa da koyo a Zamfara,” in ji Gajam.
“Muna son kowane yaro a wannan jihar ya sami koyarwa ta malami mai ƙwarewa don samun nagartaccen Ilimi.”
Gajam ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da rukunin farko na malamai 250 don samun horo nan take.
A cewar sa za a horar da sauran malamai 750 a matakai na gaba har sai an kammala dukkan 1,000.
Ya ƙara da cewa ma’aikatar sa za ta tabbatar da cewa kowane malami a jihar ya sami horon ƙarin sabbin makamar koyarwa a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin sake fasalin ɓangaren ilimi.
Kwamishinan ya ce za a ci gaba da shirin a dukkan ƙananan hukumomi 14 don tabbatar da samun dama ga kowa da kowa.
“Za a tura masu horarwa zuwa ƙananan hukumomi don rage katsewar ayyukan aji”.
Ya yi kira ga malamai da su goyi bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnati a ƙarƙashin ajandar Gwamna Dauda Lawal na shirin ceton Jihar, yana mai kira a garesu da su cigaba da jajircewa kan manyan nauyin da ke kansu.
“Malamai su ne ginshiƙin kowane tsarin ilimi. Muna roƙonku da ku bi manufofin gwamnati, ku yi aiki tuƙuru, kuma ku sauke nauyin da ke kanku da himma,” in ji shi.
Ma’aikatar Ilimi, jimiyya da fasaha ta ce za a fitar da cikakkun bayanai game da jadawalin horon, masu gudanarwa, da wuraren aiki ga dukkan sakatarorin ilimi a matakin ƙananan hukumomi nan ba da jimawa ba.
Kwamishinan ya bayyana matakin a matsayin wani mataki mai kyau na magance giɓin koyo da rashin tsaro da ƙarancin malamai a jihar.
