‘Yan bindiga sun kashe wani babban manomi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

‘Yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa kuma babban manomi Alhaji Bala Sani Kawo bayan da ya biya Naira miliyan biyar kuɗin fansa a ƙaramar hukumar Dandume.

Haka na zuwa me bayan da ‘yan bindigan suka kashe Manjo Janaral Rabe Abubakar mai ritaya a wajen yankin Matazu.

Yanzu haka dai rundunar sojoji sun ƙaddamar da hare hare a inda maɓoyan ‘yan bindaga musamman a yankin Matazu inda aka kashe Janaral Rabe Abubakar kuma har yanzu mai ɗakin sa na hannun ‘yan bindigan da ke yankin.

A kwanakin nan hare haren ‘yan bindiga ya zafafa a sassan jihar inda cikin kwanaki biyu wata majiya ta nuna cewa ‘yan bindiga sun kai hare hare har sau 11 a faɗin jihar.

Yanzu dai mafi yawan mutane masu ababen hawa sun ƙauracewa hanyoyin Katsina zuwa Dutsinma har ta mike zuwa mararrabar Ƙankara da kuma hanyar Charanchi zuwa mararrabar Musawa waɗanda suke manyan hanyoyi ne da suka haɗe zuwa wasu jihohi.

Haka ma da yawa ƙananan hukumomin da akai yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga ya warware sakamakon komawa ruwa da ‘yan bindigan suka yi.

By ukarofi

Leave a Reply