Daga UMAR GARBA a Katsina
Dakarun rundunar sojin Najeriya na Operation FANSAN YANMA sun ceto matar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar, Amina Abubakar, bayan arangama da ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa majiyoyin soji sun bayyana wa Zagazola Makama, cewa an gudanar da aikin ceton ne bayan wani samame na bayanan sirri ƙarƙashin Operation CLEAN SWEEP III, wanda aka ƙaddamar bayan sace tsohon jami’in sojin da iyalansa.
Rahotanni sun ce dakarun sun yi artabu da ‘yan bindigar a ƙauyen Tunga, inda maharan suka harbi matar kafin su tsere sakamakon matsin lambar da sojoji suka yi musu.
An ba matar agajin gaggawa a wurin kafin a garzaya da ita asibiti domin ci gaba da kula da lafiyarta.
Sojoji sun ce sun ƙara ƙaimi wajen bibiyar maharan da ake zargin suna da hannu a harin da kuma sace-sacen, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da rushe maɓoyar masu laifi a yankin.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita tare da mijinta marigayi a ranar 30 ga watan Mayun 2026.
Maharan sun kai musu farmaki ne a kan hanyar marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina, a lokacin da suke tafiya domin halartar wani ɗaurin aure.
