NDC ta zaɓi Mustapha Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jam’iyyar NDC ta zaɓi Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano.

Wannan mataki ya biyo bayan wani shiri na jam’iyyar na tsara sahun ‘yan takararta gabanin zaɓukan da ke tafe, musamman a jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya Scholars, Dr. Mansur Hassan Kumbotso, ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da Freedom Radio Kano.

Ana sa ran jam’iyyar za ta fitar da ƙarin bayanai kan yadda aka cimma wannan matsaya da kuma shirye-shiryen da take yi na tunkarar zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply