
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An tabbatar da rasuwar Mai Garin ƙauyen Olayinka da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, Oba Salman Olatunji Aweda bayan waɗanda suka sace shi sun nemi a biya fansar Naira miliyan 21, sabbin babura guda biyu da jarkan fetur a matsayin sharuɗɗan sako shi.
A cewar jaridar ShaharaReporters, an tabbatar da labarin ne a wani saƙon faifan murya daga wani mamban kwamitin da aka samar don ƙoƙarin ceton marigayin sarkin.
A saƙon, mamban ya sanar da abin alhinin ne ga ‘yan garin Olayinka, ina ya bayyana rashin basaraken a matsayin “ikon Allah” duk da yunƙurin da makusanta, ‘yan garin da jagororin addini na neman a sako shi cikin aminci.
Mamban ya kuma ce dukkan wata jita-jita da ake yi akan makomar sarkin ta zo ƙarshe tunda an tabbatar da rasuwarsa, yana mai cewa baki ɗaya yunƙurin ceto shi bai yi nasara ba.
Kazalika, ya yi kira ga ‘yan ƙauyen da su karɓi al’amarin a matsayin ƙaddara, yana mai cewa tuni aka shirya yi wa basaraken Salatul-Gha’ib kasancewar ba a samu gawarsa ba.
Wani da ya shaƙi iskar ‘yanci da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Sagbe na jihar, ya bayyana cewa basaraken ya rasu tun a hannun ‘yan bindigar duk da cewa iyalan nasa sun kai kafin-alƙalamin kuɗin fansar da ‘yan bindigar suka buƙata.
