Gwamna Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na kawo ƙarshen ta’addanci a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

“Zamu cigaba da aiki kafaɗa kafaɗa don Kawo karshen ta’addanci a Jihar Katsina” inji Malam Dikko Raɗɗa

Gwamnan yayi wannan bayanin ne yayin da ya karɓi baƙuncin Mataimakin Sufeto Janar na ’yan sanda (DIG), Dr. Muhammad Sulaiman, mai wakiltar shiyyar Arewa maso Yamma kuma mai kula da sashin kuɗi na rundunar ’yan sandan Najeriya, a wata ziyarar aiki da ya kai gidan gwamnatin Jihar Katsina.

Wannan ziyara ta biyo bayan ganawar da Gwamna Raɗɗa ya yi da Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IG Olatunji Rilwan Disu, a Abuja, kuma wani mataki ne na ci gaba da inganta haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da rundunar ’yan sandan Najeriya wajen magance matsalolin tsaro da ya addabar jihar.

A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun nazarci halin tsaro a faɗin jihar tare da tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai, musayar bayanan sirri da daidaita ayyukan jami’an tsaro domin ƙara kaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Gwamna Raɗɗa ya yabawa mataimakin sufeto janar da ɗaukacin rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa jajircewarsu da sadaukarwar da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.

Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya, yana mai bayyana cewa ɗorewar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro shi ne mabuɗin samun zaman lafiya mai ɗorewa, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma dawo da cigaban tattalin arziki da zamantakewa a faɗin Jihar Katsina.

Ziyarar ta sake nuna ƙudirin gwamnatin jihar Katsina da rundunar ‘yan sandan Najeriya na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen daƙile matsalolin tsaro da tabbatar da zaman lafiya da walwalar al’ummar jihar.

Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Alh. Abdulkadir Mamman Nasir, Babban Sakataren Gwamna, Hon Abdullahi Aliyu Turaji, Kwamishinan Tsaro na jihar Katsina, Alh Nasuru Mu’azu Danmusa, Mataimakin Sufeton Yan Sanda na Zone 14, AIG Bello Shehu, Kwamishinan Yan Sanda na jihar Katsina, CP Umar Ali Fagge da sauran jami’ai daga rundunar ‘yan sanda.

By ukarofi

Leave a Reply