Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Daga satar shanu da hare-haren karkara, matsalar ’yan bindiga a Nijeriya ta rikiɗe zuwa wata babbar masana’antar aikata laifuka da ta haɗa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, kai hare-hare kan ƙauyuka, karɓar haraji daga al’umma da kuma tilasta wa dubban mutane barin muhallansu.
A yankunan Arewa maso Yamma, dazuzzukan da suka mamaye jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da wasu sassan Kaduna sun zama mafaka ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke kai hare-hare kan matafiya da ƙauyuka kafin su koma cikin dazuzzukan.
Rahoton cibiyar bincike ta SBM Intelligence ya nuna cewa tsakanin Yulin 2024 zuwa Yunin 2025, an yi garkuwa da mutane aƙalla 4,722 a faɗin Nijeriya, yayin da aka biya kuɗin fansa da suka kai sama da Naira biliyan 2.57, duk da cewa jimillar kuɗin da masu garkuwar suka nema ta zarce Naira biliyan 48. Rahotanni sun kuma nuna cewa dubban mutane sun rasa rayukansu a maɓoyar masu garkuwa da mutane a cikin ’yan shekarun nan.
Matsalar tsaro ta bazu daga Arewa maso Yamma zuwa wasu sassan Arewa ta Tsakiya, inda rikice-rikicen manoma da makiyaya, faɗace-faɗacen ƙabilanci, hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da jama’a suka zama ruwan dare. Jihohin Neja, Benuwe, Filato, Nasarawa, Kwara da wasu sassan Kogi sun sha fama da hare-hare kan ƙauyuka da makarantu.
A yau, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa ta zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu aikata laifuka. Abin da ya fara da kai hare-hare kan masu hannu da shuni ya rikiɗe zuwa wata ƙaƙƙarfar hanyar kasuwancin laifi da ke shafar ɗalibai, sarakuna, ’yan siyasa, malamai, ’yan kasuwa, jami’an tsaro da talakawa.
Sabuwar matsalar da ta sake jawo hankali ita ce garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a jihar Katsina. Wannan lamari ya sake nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a ƙasar.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda manyan hafsoshin soja da tsofaffin jami’an tsaro suka shiga cikin jerin wadanda aka kashe ko aka yi garkuwa da su. A cikin shekaru takwas da suka gabata, aƙalla manyan hafsoshin soja goma sun fuskanci irin waɗannan hare-hare.
Manjo Janar Mohammed Idris Alƙali:
Marigayi Manjo Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya) ya kasance Babban Jami’in Gudanarwa a Hedikwatar Sojin Nijeriya da ke Abuja. An bayyana ɓatansa a ranar 3 ga Satumban 2018 kafin daga bisani a gano gawarsa a ranar 31 ga Oktoban shekarar.
Yayin da yake tafiya daga Abuja zuwa gonarsa a jihar Bauchi, ya tsinci kansa cikin wani rikici a yankin Jos ta Kudu na jihar Filato. Rahotanni sun nuna cewa wasu fusatattun matasa sun tare shi, suka gane shi jami’in soja ne sannan suka kashe shi.
Bayan bincike mai zurfi da Sojojin Nijeriya suka gudanar, an gano gawarsa a cikin wata tsohuwar rijiya a yankin Guchwet da ke Jos ta Kudu. Daga baya an binne shi a maƙabartar Gudu da ke Abuja.
Air Chief Marshal Aleɗ Badeh:
Tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Air Chief Marshal Aleɗ Badeh (mai ritaya), ya rasa ransa a ranar 18 ga Disamban 2018 lokacin da wasu mahara suka buɗe masa wuta a kan hanyar Abuja zuwa Keffi.
An kashe shi tare da direbansa yayin da yake dawowa daga gonarsa. Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamin Babban Hafsan Sojin Sama sannan daga bisani ya zama Babban Hafsan Tsaro a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Air ɓice Marshal Muhammad Maisaka:
A ranar 8 ga Nuwamban 2021, wasu ’yan bindiga sun kashe Air ɓice Marshal Muhammad Maisaka (mai ritaya) tare da jikansa a gidansa da ke Rigasa a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Marigayin ya kasance tsohon Daraktan Horarwa da Ayyukan Likitanci a Hedikwatar Tsaro.
Kanal Rabi’u Garba Yandoto:
A ranar 1 ga Janairun 2023, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da Kanal Rabi’u Garba Yandoto (mai ritaya) tare da ’ya’yansa biyu a hanyar Gusau zuwa Tsafe a jihar Zamfara.
Masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 50 kafin daga baya aka rage kuɗin. A ranar 10 ga Janairun 2023, an sake shi tare da ’ya’yansa bayan an biya kuɗin fansa da aka ce ya kai kusan Naira miliyan 10.
Manjo Janar Richard Duru:
An yi garkuwa da Manjo Janar Richard Duru mai ritaya a Owerri, jihar Imo, a watan Satumban 2023.
Duk da rahotannin cewa an biya dala 50,000 domin a sake shi, daga bisani masu garkuwar suka kashe shi. Rundunar ’Yan Sandan jihar Imo ta ce ta kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Birgediya Janar Uwem Udokwere:
A ranar 22 ga Yunin 2024, wasu ’yan fashi da makami sun kutsa gidansa a Sunshine Homes Estate da ke Lokogoma a Abuja, inda suka kashe Birgediya Janar Uwem Harold Udokwere (mai ritaya).
Rahotanni sun nuna cewa an daba masa wuƙa ne yayin da yake ƙoƙarin kare iyalinsa. Daga baya ’yan sanda suka cafke wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Birgediya Janar Maharazu Tsiga:
Tsohon Darakta Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya shiga hannun masu garkuwa a ranar 5 ga Fabrairun 2025 a garinsu Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
An yi garkuwa da shi tare da wasu mutum tara, yayin da aka kashe mutum guda. Bayan kwanaki 56 a hannun masu garkuwa, an sake shi a ranar 3 ga Afrilun 2025.
Manjo Joe Ajayi:
ɗaya daga cikin mafi muni shi ne na Manjo Joe Ajayi mai shekaru 76.
An yi garkuwa da shi a gidansa da ke Odo-Ape a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi a ranar 21 ga Mayun 2025.
Ko da yake iyalansa sun biya Naira miliyan 10 a matsayin fansa, ya rasu a hannun masu garkuwar kafin a sake shi.
Kanal Joseph Ajanaku:
A watan Janairun 2026 ne aka yi garkuwa da Kanal Joseph Ajanaku (mai ritaya) daga gidansa da ke jihar Filato.
Masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 200 tare da yin barazanar kashe shi. Sai dai jami’an tsaro sun gudanar da wani samame cikin sirri tare da kuɓutar da shi a wannan rana.
Manjo Janar Rabe Abubakar:
Shine sabon wanda ya shiga wannan jerin. A ranar 30 ga Mayun 2026, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Nijeriya, tare da matarsa suna kan hanyarsu zuwa ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina lokacin da wasu ’yan bindiga suka tare motarsu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da ma’auratan, yayin da direbansu ya tsira duk da harbin bindiga da ya samu.
Rundunar ’Yan Sandan jihar Katsina ta tabbatar da harin, tana mai cewa maharan sun buɗe wuta kan motar kafin su sace ma’auratan.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Manjo Janar Abubakar da matarsa na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane. Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun fara tuntuɓar iyalansu tare da gabatar da wasu sharuɗɗa domin sakin su.
