
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta shirya ƙaddamar da adaidaita sahu masu amfani da lantarki guda 10,000 a matsayin wani shiri na sauƙaƙe lamuran sufuri a Nijeriya da kuma bunƙasa harkokin fannin.
Hukumar kula da Ci-gaban Shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) ne za ta jagoranci raba adaidaitan a watan Agustan 2026 domin amfanin al’umma a shiyyar da ma wasu sassa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya bayyana haka yayin wani zama da Ƙungiyar ‘Yan Sufuri masu goyon bayan Tinubu/Shettima a 2027 a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce shugaban ƙasar ya amince da maimaita irin shirin a wasu sassan Nijeriya ta hukumomin ci-gabansu.
Ya ce, gwamnatin Shugaba Tinubu tana fifita harkokin ci-gaba a Nijeriya don haka ya sa take ƙoƙarin zamanantar da lamuran sufuri a tashoshin jiragen ruwa, na jiragen ƙasa da na sama da motoci masu amfani da iskar gas don tallafa wa lamuran kasuwanci, noma, masana’antu da kuma kusanto da sassan ƙasar.
Shettima ya bayyana cewa, shirin samar da sauye-sauye a fannin sufuri na gwamnatin ya samu karɓuwa ta ƙaddamar da ababen hawa masu amfani da iskar gas a manyan tashoshin jiragen ruwa, lamarin da ya taimaka wajen inganta harkokinsu.
Haka kuma, ya ce gwamnatin tana ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga sufurin ababen tattali ta hanyar rage cinkoso, jinkiri, sadar da manoma da kasuwanni, inganta samar da kayayyaki da kuma ba masu ayyukan sufuri yanayin mai kyau na gudanar da harkokinsu cikin tsarin ci-gaba.
Kazalika, Shettima ya tabbatar wa masu ayyukan sufuri cewa Gwamnatin Tarayyar za ta cigaba da tallafa wa tsare-tsaren da za su taimaka wajen samun sauƙin farashin fetur, fagagen inshorar ababen hawa, kwangilolin bankuna da yanayin aiki mai kyau.

