Gwamna Raɗɗa ya ziyarci Amina Rabe da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina,Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ziyarci Hajiya Amina Rabe Abubakar, matar Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, a asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina.

Gwamnan, tare da darakta janar na sashen yaɗa labarai, Maiwada Dammallam, ya kai wannan ziyara ne bayan nasarar wani samame da rundunar soji ta gudanar wanda ya tabbatar da samun ‘yancinta. Dakarun Operation FANSAN YANMAN sun yi artabu da ‘yan bindiga tare da ceto ta cikin gaggawa da ƙwarewa.

Gwamna Raɗɗa ya gode wa jami’an rundunar sojin Najeriya bisa ƙwarewa da jajircewarsu wajen gudanar da aikin ceton.

Ya yaba da jarumtaka da sadaukarwar da suka nuna wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Katsina.

Haka kuma, ya bayyana cewa jami’an Operation FANSAN YANMAN sun nuna irin jarumtaka da ƙwarewar aiki da ke ƙara wa al’ummar Katsina fata da ƙwarin gwiwa a yaƙin da ake yi da rashin tsaro.

By ukarofi

Leave a Reply