‘Yan sanda sun ƙaddamar da kama motoci masu rufaffun allunan lambobi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda ta fara gudanar da atisayen kama motoci masu ɗauke da allunan lambobi da aka rufe da waɗanda suka ƙoƙe da marasa rajista.

Hukumar ta ɗauki matakin ne domin inganta lamuran tsaro da tabbatar da rajistar ababen hawa da kuma shafe ayyukan ta’addanci a sassan Nijeriya.

Hakan na zuwa ne bisa umarnin Sufeto Janar na rundunar, Tunji Disu da nufin ƙarfafa tsaon al’umma da kuma hana miyagu amfani da ababen hawa da ba su da rajista ko asali.

Tuni dai rassan rundunar na jihohi suka fara aiwatar da umarnin, inda suka gargaɗi jama’a da cewa duk wanda aka samu da laifin sufuri da abar hawa mara rajistar ko rashin samun bayyannen allon lamba, za a kama shi tare da maka shi a kotu don ya fuskanci hukuncin doka.

Wasu daga cikin jihohin sun haɗa da Kogi, Delta da Ribas, inda rundunonin suka gargaɗi al’umma akan al’amarin musamman ganin yadda miyagun laifuka da suka shafi garkuwa da munanan hare-hare suka yawaita a sassan Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply