Gwamna Lawal ya yaba wa masu yiwa ƙasa hidima a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa masu yiwa ƙasa hidima da aka turo Jihar saboda rawar da suke takawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai bayyana aikinsu a matsayin ma’aikatan wucin gadi na hukumar zaɓe ta ƙasa INEC a matsayin muhimmin abu ga zaɓe mai inganci a zaɓen 2027.

Gwamnan ya yi wannan yabo ne yayin da yake bude kwas na gabatarwa na rukunin ‘B’ Stream I na 2026 a sansanin horar da matasa na NYSC da ke Gusau.

Sakataren dindindin na na’aikatar matasa da wasanni, Alhaji Nasiru Galadima Kaura ne ya wakilce shi.

Gwamna Lawal ya buƙaci mambobin da aka turo a matsayin jami’an INEC da su gudanar da ayyukansu da himma, mutunci, kishin ƙasa.

Ya ce halayensu zai zama muhimmi wajen tabbatar da zaɓe mai zaman lafiya, adalci da sahihanci, da kuma ci gaba da zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

Gwamnan ya kuma taya NYSC murnar cika shekaru 53 da kafuwa, yana mai kiran shirin a matsayin ɗaya daga cikin shirye-shiryen gina ƙasa mafi nasara a Najeriya.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa tare da ƙarfafa mambobin ƙungiyar su shiga cikin dukkan ayyuka a sansanin su.

Tun da farko, kodinetan NYSC na Zamfara, Mallam Muhammad Lawan Ahmed, ya ce bikin rantsar da membobin ƙungiyar a hukumance yana karɓar membobin ƙungiyar kuma yana taimaka masu don kammala yiwa ƙasa hidima cikin nasara.

Ya roƙe su da su yi amfani da koyarwar makonni uku don haɓaka ƙwarewar jagoranci da kuma samun horo mai dacewa na shekarar hidimar ƙasar su.

Babban alƙalin Jihar Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu, ce ta gudanar da rantsuwar wanda mataimakiyar magatakarda Aishatu Jibrin ta wakilta.

By ukarofi

Leave a Reply