Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta kara zuba jari a ci gaban Ilimin ƙananan yara na farko, ECD, tana mai cewa koyon wasa yana da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa nishadi da ƙwarewa ga yara ƙanana da kuma bunƙasa ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci.
Hukumar ta yi wannan kiran ne a ranar Litinin ta hannun mai taimakawa UNICEF na ƙasa a fannin ECD, Dr. Adamu Gaya, yayin ayyukan bikin Ranar Wasan Yara ta duniya a makarantar Smart School da ke Gusau.
An shirya taron ne tare da haɗin gwiwar hukumar bada Ilimi bai ɗaya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB.
Taron ya haɗa iyaye, masu kula da yara, masu ruwa da tsaki kan ilimi, jami’an ZSUBEB, da wakilan UNICEF don wayar da kan ɗalibai kan alaƙar da ke tsakanin ilimi, koyo, da wasanni.
Dr. Gaya, wanda ke kula da horar da ECD a faɗin jihohin Sokoto, Kebbi, da Zamfara, ya ce Ranar Wasan Duniya, wadda ake gudanarwa a duk duniya a ranar 11 ga Yuni, tana ba yara ‘yancin bayyana kansu yayin da take ƙarfafa dabarun ci gaban Ilimi.
“Wasan yana ba wa yara damar haɓaka baiwa da iyawarsu a fannoni daban-daban, yana taimaka musu su girma su zama mutane masu himma, masu ƙwarewa waɗanda za su iya ba da gudummawa mai ma’ana ga al’umma,” in ji shi.
Ya gano muhimman fannoni guda shida da aka inganta ta hanyar koyo bisa ga wasa: fasahar ƙere-ƙere, iyawar fahimta, haɓaka harshe, ci gaban jiki, da hulɗar zamantakewa da farin ciki a tsakanin yara.
A cewarsa, shirin ya yi daidai da tsarin ilimi na duniya, gami da Ilimin fasaha da horarwa, TVET, wanda ke ba da fifiko ga ƙwarewar aiki da ƙirƙira tun daga ƙuruciya.
Dr. Gaya ya jaddada cewa saka hannun jari a ilimin yara yana da alaƙa kai tsaye da ci gaban ƙasa da wadatar tattalin arziki.
“Ci gaban tattalin arziki yana da alaƙa da saka hannun jari a ilimin yara ƙanana, kamar yadda aka bai wa mutane da yawa masu nasara damar haɓaka baiwarsu tun suna ƙanana,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnatin Zamfara da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da samar da isassun kuɗade da faɗaɗa shirye-shiryen da suka dogara da wasa don ba wa yara a jihar damar yin gasa a duniya.
Shugaban hukumar bada Ilimi bai ɗaya na jihar Zamfara ZSUBEB, Farfesa Nasiru Garba Anka, ya nanata alƙawarin hukumar na samar da ilimi mai haɗaka da jan hankali ga dukkan yaran Zamfara.
Ya ce shirya ayyukan da suka shafi wasanni wani ɓangare ne na dabarun hukumar don tabbatar da ci gaban jiki, da tunani na ɗalibai.
“Shirya irin waɗannan ayyukan wani ɓangare ne na babban dabarun ZSUBEB don tabbatar da ci gaban jiki da tunani na yara,” in ji Farfesa Anka.
Shugaban ZSUBEB ya bayyana shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan Ranar Wasan Duniya ga makarantu a duk ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Ya kuma yi kira ga makarantu na gwamnati da masu zaman kansu da su rungumi hanyoyin koyarwa waɗanda ke haɗa koyo da wasa.
Farfesa Anka ya yaba wa UNICEF saboda kyakkyawan goyon bayanta mai tasiri kuma ya nuna kyakkyawan fata game da ƙarfafa haɗin gwiwa don inganta ilimin yara ƙanana a Jihar ta Zamfara.
