‘
Daga UMAR GARBA a Katsina
Kwanaki biyu bayan mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar a hannun ‘yan bindiga, wata dabar ‘yan bindiga a Katsina ta kashe Alhaji Bala Sanin Kawo, wani fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a a ƙaramar hukumar Ɗandume ta jihar.
Jaridar Blueprint ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kashe shi ‘yan sa’o’i bayan sun karbi kuɗin fansa na Naira miliyan 500 daga hannun ‘yan uwansa.
Alhaji Kawo yayi fice a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan kasuwa mafi shahara da tasiri a Arewacin Najeriya, musamman gudunmawar da ya bayar a ɓangaren noma, ci gaban al’umma, da kuma ayyukan jin ƙai.
Rahotannin sun bayyana cewa ana zargin ‘yan bindiga ne suka sace shi ‘yan makonni da suka gabata kuma daga baya ‘yan bindigar sun nemi a biya su kudin fansa kafin su sake shi.
Wasu rahotanni sun gano cewa an tattara kuɗin ne daga ‘yan uwa da abokan arziki aka kai wa ‘yan bindigar a maɓoyarsu amma duk da haka sai da suka kashe mutumin bayan sun karbi kuɗin fansa.
Mutuwar ɗan kasuwar mai taimakon jama’a ta haifar da sabon damuwa game da taɓarɓarewar tsaro a jihar Katsina, inda sace mutane don neman kuɗin fansa ke ci gaba da zama babbar barazana ga rayuwar al’umma.
Mazauna yankin da masu ruwa da tsaki sun yi kira ga hukumomin tsaro da hukumomin gwamnati da su ƙara himma wajen magance barazanar fashi da makami da satar mutane a faɗin ƙasar.
Ƙaramar hukumar Ɗandume na ɗaya daga cikin yankuna tara da al’ummomi ba sa barci da idanunsu a rufe tsawon shekaru takwas da suka gabata.
Kwanan nan, Gwamna Umar Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta amince za ta tattaunawa da ‘yan bindigar da suka tuba don samun zaman lafiya a faɗin jihar.
