
Rundunar ‘Yan Sanda a Abuja, ta kama wata mata mai juna biyu, Hauwa Shafi’u da wasu mutum uku da ake zargi da alaƙa da masu garkuwa da mutane a yankin Byazhin da ke kusa da birnin tarayyar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Birnin Tarayya, Ahmed Sanusi, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai a maɓoyar ‘yan bindiga a ranar 11 ga watan Yuni, inda aka kashe wasu daga cikin masu laifin tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
A cewarsa, Hauwa Shafiu na samar wa ƙungiyar kayan masarufi tare da dafa musu abinci, duk da kasancewarta cikin matsanancin ciki.
Sanusi ya bayyana cewa bayan kama ta, rundunar ta garzaya da ita asibiti inda daga bisani ta haifi jariri. Ya tabbatar da cewa ita da jaririn suna cikin koshin lafiya kuma suna samun kulawar da ta dace.
Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da Yahaya Abdullahi, Muhammed Yunusa da Shamsudeen Mustapha. Bincike ya nuna cewa suna cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke tattara bayanai da shirya hare-hare a yankunan da ke kusa da Abuja.
Rundunar ta kuma ce, ta ƙwato babura huɗu, ƙwayoyin tramadol, wayoyi biyar, na’urar POS, kayan girki da kuma kuɗi Naira 320,000, waɗanda ake zargin sun fito ne daga kuɗin fansar wani mutum da aka yi garkuwa da shi.
Kwamishinan ƴan sandan ya ce ana ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere, tare da ɗaukar matakan rushe maboyar masu aikata laifuka a yankin.
