An zargi sojojin sama da lakaɗa wa direba dukan da ya yi ajalinsa bisa ɓata motarsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani direban motar kasuwa ƙirar bus mai suna Joseph Okpe ya rasu bayan zargin jami’an sojin sama da casa shi akan wani rikici yayin ƙaramin cinkoson ababen hawa da ya haɗa da motarsu a hanyar Oshodi zuwa Apapa da ke Jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2026 kamar yadda bayanan ƙorafin da aka yi a Babbar Kotun Abuja suka bayyana, inda aka zargi cewa marigayin mai shekaru 43 ya daku ne bayan tsama akan damejin wata mota ta jami’an sojojin.

A cewar takardar ƙorafin da ɗan uwan mamacin, Innocent Okpe ya shigar, al’amarin ya faru ne a lokacin da marigayin ke gudanar da aikinsa na kabu-kabu, inda ya yi arangama da jami’an da ke tafiya a wata motar bus.

Jami’an sun zarge shi da kartar motar da suke ciki, lamarin da ya sa suka nemi ya biya diyyar N100,00 a matsayin horo a gare shi.

Kasancewar Okpe ya gaza samar da kuɗin, sai suka shiga dukan sa har ta kai ga sun masa jina-jina a fuska da kansa, lamarin da ya yi sanadiyyar fita a hayyacinsa.

A cewar jawabin ƙorafin, jami’an sun daina lakaɗa nasa dukan ne a lokacin da wasu abokan aikinsa da masu wucewa suka shiga tsakani wajen roƙon jami’an akan su ƙyale shi.

Haka kuma, ya ce sai da aka yi wa jami’an karo-karon N50,000 a matsayin diyyar damejin motar tasu kafin suka bar shi.

Wani shaida ya ce, bayan haka ne aka garzaya da shi asibitoci da dama suka ƙi karɓar sa, sai da aka kai shi asibitin Charing Cross Clinic a yankin Mushin, inda aka sanar da rasuwarsa da kwatankwacin ƙarfe 5 na yamma.

By Babaji

Leave a Reply