Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Sufeto Janar na ’Yan sanda, IGP Olatunji Railwan Disu, a yau Talata ya jagoranci sallar jana’iza ga jami’ai uku da bom ya kashe a kan hanyar Anka zuwa Bagega, yayin da ya isa Gusau domin tattaunawa ta musamman kan yadda ta’addanci yake ƙaruwa a jihar.
An gudanar da sallar jana’izar ne a hedikwatar ’yan sandan jihar Zamfara da ke Gusau, kuma babban limamin masallacin Juma’a na hedikwatar, CSP Sulaiman Alhassan, ne ya jagoranta.
Jami’an uku sun mutu a yammacin ranar Litinin lokacin da sukaje don kwance wani bom da ’yan bindiga suka dasa a kan hanyar Anka zuwa Bagega.
Wannan hari na daga cikin hare-haren da suka fi muni da aka kai wa jami’an tsaro a Zamfara a bana.
A jawabi mai cike da baƙin ciki bayan kammala sallar, IGP Disu ya bayyana lamarin a matsayin “abun takaici da rashin imani.
“Za a gano masu aikata wannan laifin nan ba da jimawa ba, kuma za su fuskanci fushin doka,” in ji IGP din.
Ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara, rundunar ’yan sandan jihar, da iyalai na jami’an da suka mutu, yana addu’ar Allah ya jiƙansu ya kuma bai wa iyalansu haƙuri.
“’Yan sanda ƙarƙashin jagorancina za su ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro don murƙushe mafakar ’yan ta’adda a Arewa maso Yamma da faɗin ƙasar nan,” in ji Disu.
Manyan jami’ai da suka halarci jana’izar sun haɗa da kwamishinan ’yan sandan jihar, CP A.M Bello, sakataren gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Nakwada, manyan jami’an sojin Najeriya, Hukumar Shige da Fice, FRSC, hukumar gyaran hali, hukumar kwastam, da kuma NSCDC. Kasancewar shugabannin dukkan hukumomin tsaro ya nuna girman wannan hari da kuma haɗin kan jami’an tsaro.
Ziyarar ta IGP Disu zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara, na daga cikin shirye-shiryen daidaita hare-haren ’yan bindiga da suka sake ƙaruwa a jihar.
An tarbeshi a filin jirgin sama na Gusau wanda sakataren gwamnatin jihar SSG Nakwada, CP A.M Bello, shugabannin rundunonin soja, da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarta.
Blueprint Manhaja ta tattaro cewa ziyarar ta biyo bayan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a tsakanin al’ummomi da dama, musamman a yankunan Anka, Bagega, Maru, da Zurmi.
Ya bayyana cewar zai mai da hankali kan nazarin ayyukan da ke gudana, kimanta dakaru na musamman, da gabatar da dabaru masu dogaro da bayanan sirri domin murƙushe sansanonin ’yan bindiga da katse hanyoyin samar musu da kayayyaki.
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Nakwada, wanda ya tarbi IGP a madadin Gwamna Dauda Lawal, ya tabbatar wa shugabancin ’yan sanda goyon baya cikakke na gwamnatin jihar.
“Zamfara ta ƙuduri aniyar aiki tare da dukkan hukumomin tsaro domin mayar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Muna maraba da ziyarar IGP a wannan lokaci mai mahimmanci kuma mun shirya bayar da dukkan kayayyaki da tallafi ga hukumomin tsaro don inganta ayyukan su na yaƙi da yan ta’adda,” in ji SSG .
Ya ce gwamnatin jihar ta ƙara ƙarfafa haɗin kai da hukumomin tsaro na tarayya da kuma tattara bayanan sirri na cikin gida.
