An sallami fasinjojin da hatsarin jirgin ƙasan Warri zuwa Itakpe ya rutsa da su daga asibiti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Baki ɗaya fasinjojin da suka jikkata yayin hatsarin jirgin kasa na 8 ga watan Yuni a hanyar Warri zuwa Itakpe sun bar asibitocin da aka yi musu jinya.

Haka kuma, an samo dukkan ababen da hatsarin ya rutsa da su.

Darakta-Manaja kuma Shugaban Hukumar kula da Harkokin Jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC), Kayode Opeifa ya sanar da haka a wata takarda, ranar Talata a Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN, ya ruwaito cewa, hatsarin jirgin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:17 na ranar, a kusa da tashar jiragen ƙasa na Goodluck Jonathan da ke Agbor a Jihar Delta, wanda ya rutsa da rassansa huɗu.

Sannan, al’amarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke ɗauke da fasinjoji 442, jami’an gudanarwa 40, jami’an tsaro, jami’an lafiya, masu shara, masu dafa abinci da wasu ma’aikata.

An ruwaito cewa, mutane biyar ne suka rasu sakamakon faruwar al’amarin, inda aka gaggauta garzayawa da waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitoci a Agbor da ƙauyuka da ke kusa da yankin.

A cewar shugaban na NRC, hukumar tana mai jajenta wa iyalan mamatan kuma za ta cigaba da kasancewa tare da su a yayin jimamin al’amarin.

Ya kuma yi godiya ga hukumar gudanarwa da tawagar lafiya ta asibitocin da suka karɓi kulawar waɗanda abin ya shafa bisa ƙwarewa da sadaukarwa.

By Babaji

Leave a Reply