Sojoji sun ceto wasu da aka sace su tare da daƙile yunkurin garkuwa da mutane a Katsina da Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sojojin sashe na 2, Operation FANSAN YAMMA, sun ceci mutane bakwai da aka sace tare da daƙile yunƙurin sace wasu a ayyuka daban-daban a faɗin jihohin Katsina da Zamfara, in ji rundunar haɗin gwiwa (Arewa maso Yamma).

An gudanar da ceton ne ta hanyar ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci da bincike da ceto da nufin kawar da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma,

A cewar wata sanarwa daga Laftanar Kanar Aliyu Danja, jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ya ce an ceto waɗanda aka sace mutum huɗu a Katsina A Lokacin aikin kakkaɓe yan ta’adda watau Operations Sweep 3′.

“A ranar Litinin, 16 ga Yuni, sojoji sun gudanar da Operation Clean Sweep 3, sun ƙara tsananta hare-haren kan yankunan ‘yan ta’adda a yankin ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.” An tsara wannan aikin ne don ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar kwanan nan ta hanyar wargaza hanyoyin sadarwa na ‘yan ta’adda da kuma ‘yantar da waɗanda suka yi garkuwa da su”

Sojoji sun kai hari kan wata maɓoyar ‘yan ta’adda da aka gano a ƙauyen Fafu, ƙaramar hukumar Matazu. Bayan harin da aka kai musu da kuma karfin bindiga mai ƙarfi, ‘yan ta’addan sun bar sansaninsu tare da waɗanda aka sace kafin su gudu.

Sojoji sun share sansanin kuma sun ceto mutane huɗu da aka sace waɗanda a halin yanzu suna karɓar kulawar lafiya saboda raunukan da suka samu a lokacin da aka sace su.

A wani lamari makamancin haka a jihar Zamfara, sojojin da aka tura a garin Zurmi, ƙaramar hukumar Zurmi, sun daƙile yunƙurin sace mutane bayan da ‘yan ta’adda suka kutsa kai cikin al’umma da nufin sace mazauna yankin.

A cewar sanarwar, sojojin sun amsa kiran gaggawa, inda suka yi tattaki zuwa wurin da lamarin ya faru suka fafata da ‘yan ta’addan a wani mummunan faɗa inda yan ta’addan suka gudu zuwa daji nan take.

“Bayan cikakken cin zarafin mazauna yankin, sojoji sun ceto mutane uku da aka sace kuma suka tabbatar da tsaronsu da kuma komawa ga iyalansu.”

A cewar Laftanar Kamar Danja, saurin martanin rundunar sojin ya daƙile duk wani yunƙurin yan ta’adda na satar jama’a a ƙaramar hukumar da ke fama da rikici.

Laftanar Kanar Danja ya ce nasarorin da aka samu a aikin sun nuna jajircewar Operation FANSAN YAMMA wajen kare rayuka da dukiyoyi a faɗin Arewa maso Yamma.

“Sojojin zasu ci gaba da jajircewa wajen cigaba da ayyukan kai hari a maboyar yan ta’adda don hana su duk wani ‘yancin kai gari ga alummar Jihar tare da tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya ga dukkan al’ummomin da abin ya shafa,” in ji shi.

By ukarofi