Hajjin 2024: Gwamnatin Kebbi ta fitar da Naira biliyan 3.34 don tallafa wa maniyyatan jihar 3,344

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta amince da bayar da tallafin Naira biliyan 3.34 ga maniyyata 3,344 da ke son zuwa aikin Hajjin bana daga jihar.

MANHAJA ta rawaito cewa an fitar da kuɗin ne don kammala biyan ƙarin kuɗin aikin Hajjin bana da ya kai kimanin Naira miliyan 1.9 da hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta sanar.

An cimma wannan matsayar ne a wani taron gaggawa na Majalisar Zartaswa da Mataimakin Gwamna, Umar Abubakar Tafida ya jagoranta, a Birnin Kebbi a ranar Litinin.

Da ya ke jawabi ga manema labarai kan sakamakon taron, kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Yakubu Ahmad, ya ce an yi hakan ne domin kyautatawar Gwamna Nasir Idris na ganin an tabbatar da kimar addini domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.

Ya bayyana cewa an fitar da kuɗin ne da nufin cika wa kowane maniyyaci domin a samu sauƙin biyan kuɗin aikin Hajjin na bana gaba ɗaya kafin ranar rufewa.

“A cikin kimanin ƙarin Naira miliyan 2 da NAHCON ta nema a matsayin ƙarin kuɗin tafiya, gwamnatin Kebbi ta ware Naira miliyan 1 ga kowane mahajjaci yayin da maniyyaci zai cika sauran da kansa.

“Alhazan da suka riga suka kammala biyan kuɗin aikin Hajjin, suma za su ji daɗin zunzurutun kuɗi naira miliyan 1 daga gwamnati ta basu,” in ji kwamishinan.