An kama matashi kan zargin kashe yayansa a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sanda jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Isyaku Babale, bisa zargin daɓa wa yayansa wuƙa har lahira.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar SP Ahmed Wakili ya fitar, ta ce binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuƙa wajen daɓa wa babban wansa mai suna Abubakar Ɓalewa ranar Lahadi, 31 ga watan Maris bayan cacar-baki da ta ɓarke tsakaninsu.

Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da ya faru ne, sai suka tura jami’ansu zuwa wurin, abin da ya kuma ya kai ga kama matashin mai shekara 30 wanda ke zaune a Anguwan Dawaki.

Ya ce bayan garzayawa da mutumin asibiti ne likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

Binciken da aka gudanar ya qara nuna cewa ‘yan uwan junan sun saba yin faɗa da juna ta hanyar amfani da muggan makamai, sai dai, a wannan karo, har ta kai ga rasa ran ɗaya daga cikinsu.

“Cacar-baki tsakanin ‘yan uwan ta ɓarke ne bayan da wanda ake zargin ya faɗa wa ɗan uwansa da ya kashe da ya daina shan ‘sholisho’ a ɗakinsu saboda warinsa, wannan abin ne ya janyo faxa tsakaninsu.

“Jim kaɗan bayan an shiga tsakaninsu ne, wanda ake zargin ya ruga ya ɗauko wani abu da ake kyautata zaton wuƙa sannan ya daɓa wa yayan nasa a ciki,” inji Wakili.

Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, suka shiga farautar wanda ake zargin inda har ta kai ga kama shi a Kasuwar Shanu na jihar ta Bauchi.

Wakili ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin yin cikakken bincike kan lamarin.