PSG ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin Faransa

Daga MAHDI M. MUH’D

Ƙungiyar ƙwallon koafa ta PSG ta samu kaiwa wasan ƙarshe na kofin Faransa wato French Cup bayan ƙwallon ɗaya tilo da Kylian Mbappe ya zura a ragar Rennes daren ranar Laraba a wasan daf da na ƙarshe da suka doka tsakaninsu.

A minti na 40 daf da tafiya hutun rabin lokaci ne Mbappe ya zura ƙwallon bayan tun farko mai tsaron ragar Rennes Steve Mandanda ya varar da fenaritin da tauraron na Faransa ya buga a minti na 33.

Mbappe wanda ke matsayin mafi zurawa PSG ƙwallo na taka leda ne a kakarsa ta ƙarshe a ƙungiyar bayan amincewa da komawa Real Madrid ta Sifaniya a kaka mai zuwa.

Ƙwallon ta Mbappe ta bai wa PSG damar kama hanyar yiwuwar lashe kofin na Faransa karo na 15, kuma karon farko bayan ɓarar da damarsu ta lashe kofin a 2021.

Hakazalika, ƙungiyar ta PSG na kuma harin aƙalla kofuna 3 ne cikin wannan kaka da suka ƙunshi na Ligue 1 da zakarun Turai inda yanzu haka za ta haɗu da Barcelona a wasan daf da na kusa da ƙarshe.