Gwamna Abba Kabir ya biya wa ɗalibai 6,500 kuɗin JAMB ‘yan asalin Jihar Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya biya wa ɗalibai maza da mata da suka gama sakandire ‘yan asalin Jihar Kano kuɗin jarrabawar share fagen shiga jami’a kimanin 6,500 don ci gaba da karatun su a kwalejoji da jami’o’i a ƙasar nan dama duniya gaba ɗaya.

Gwamnan wanda ya fara da godiya ga iyayen yara bisa jajircewarsu wajen bai wa yaransu tarbiyya da tsayawa don ci gaban su ta hanyar ilimi.

Maigirma Gwamna ya ce daga lokacin da aka zaɓi wannan gwamnati sun gudanar da ayyuka da dama ya zuwa yanzu, inda ya ce lokacin yaƙin neman zaɓe sun yi wa al’umma da dama alƙawarin farfaɗo da harkar ilimi idan an samu nasara.

“Ban mantawa wata shida da suka wuce mun ƙirƙiro da ɗaukar nauyin yaranmu da suka yi ƙwazo tare da ɗaukarsu da biya masu kuɗin makaranta da sauran abubuwan da ba a rasa ba.

“Samun labarin wasu ɗaliban da muka tura ƙasashen ƙetare basu samu kuɗin su ba ta fuskar matsalar canjin dala, ba mu yi ƙasa a gwuiwa ba ko bacci sai da muka tabbatar ya zuwa yanzu a sallame su babu mai bin wani abu.”

Gwamna Abba Kabir ya ce batun BESDA kuwa ya zuwa yanzu ya sa kwamiti da za su tantance su, wanda ya zuwa yanzu kuma an kammala tantance su, sai abinda ya yi saura.

“Kasancewar mun bai wa ilimi fifiko a jihar Kano ya sa wajen gabatar da kasafin kuɗin wannan shekara ya sa muka bai wa ilimi kaso mafi tsoka.”

Gwamnan ya kuma buƙaci ɗalibai maza da su ƙara ƙaimi wajen ganin sun samu dama kamar yadda mata suka yi ƙwazo don haka suma maza ana buƙatar ƙara ƙaiminsu.

Batun dawo da tsarin samar da kayan aiki kuwa gwamnan ya bada umarnin cigaba da samar da kayan aikin da suka hadar da tebura da kayan koyarwa da nan da bayan sallah za a tabbatar da tura wa kowace makaranta a jihar Kano.

“Suma malamai mun yi shirin ganin sun samu horo mai kyau tare da basu hakkokin su na alawus-alawus ɗin su da gwamnatin baya bata biyasu ba.”

A jawabin sa mai girma kwamishinan ilimi na jihar Kano Hon. Haruna Doguw ya ce mai girma gwamna yana tuntuvarsa a kodayaushe yadda za a tabbatar ɗaliban jihar Kano sun samu damar rubuta jarabawar Jamb.

Doguwa ya kuma ce a lokuta da yawa yana mamakin yadda mai girma Gwamna ya ke fin sauran gwamnonin jihohin najeriya kokari wajen gudanar da aiki tuƙuru.

Kwamishinan ya ce da irin aikin alkhairin da yake wa al’ummar jihar Kano zai bashi damar yin aikinsa na tsawon shekaru takwas tare da wucewa mataki na gaba.

Sannan Haruna Umar Doguwa ya kuma ƙara da cewa a yanzu haka gwamnan Kano cikin ƙudurinsa na ciyar da ilimi gaba a Kano ya kara wa ɗaliban makarantun kwana yawan harkar ciyarwa a faɗin jihar Kano.

Hajiya Rabi Inuwa Hussain wadda ta fara da gode wa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarinsa na tallafawa tsarin ilimi a wannan jiha don al’ummarsa su samu ilimi mai kyau.

Abba Kabir Yusuf ya kuma jinjina sauran ma’aikatan hukumar ilimi ta jihar Kano wajen ƙoƙarin da suka yi.

Bilal Muhammad Abubukar, Nahayatu Isah Garba, sun nuna godiyarsu bisa yadda mai girma Gwamna ya taimaka ɗaliban Kano 6,500 kuɗin jarrabawar JAMB da kowane fom ya kai naira 6,200.

Ɗaya daga cikin iyayen yara Sada Muhammad Idiris da ya wakilci sauran iyayen ya fara da godewa mai girma Gwamna bisa wannan ƙoƙari nasa.

Haka kuma ya ce a matsayinsu na iyayen yara ba su yi mamaki bisa ta hanyar lura da wanda zai zo ya taimaka harkar ilimi a jihar Kano.

Kazalika ya ce kamata mutane dake kewaye da kai a matsayin wanda suke son ci gaban ilimi, don haka wani sirri ne da baka sani ba, don haka ya ce suna godiya tare da fatan za a cigaba da tallafawa ilimi a jihar Kano.