Gwamna Raɗɗa ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su riƙa bayar da rahotannin tsaro cikin kula da haƙƙin kowanne ɓangare

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira ga masu kafafen sada zumunta, masu rubutun yanar gizo (bloggers), da masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet da su kasance masu kula da haƙƙi wajen bayar da rahotannin da suka shafi tsaro, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tallafa wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wasu jerin ganawa da ya yi a gidan gwamnatin Jihar Katsina tare da malamai da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnan ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ɗaukar ma’aikatan sintirin dazuka (Forest Guards) guda 1,000 domin ƙarfafa sa ido da inganta ayyukan tsaro a wuraren da ke cikin haɗari.

Gwamna Raɗɗa ya yi gargaɗi kan yaɗa bidiyoyi masu tayar da hankali da suka shafi waɗanda aka yi garkuwa da su, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa na ƙara jefa iyalansu cikin damuwa tare da iya kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro.

Haka kuma ya yi kashedi kan yadda wasu mutane ke yaɗa bidiyon waɗanda aka sace, har ma da lokutan da abin ya shafa iyayensu ko ‘yan uwansu na kusa, yana mai bayyana hakan a matsayin ɗabi’a mara kyau da ke hana nasarar ƙoƙarin haɗin gwiwa wajen tabbatar da tsaro.

“Ina kira ga masu tasiri a kafafen sada zumunta da masu rubutun yanar gizo da su taka rawar gani cikin gaskiya da kishin ƙasa wajen magance matsalar rashin tsaro. Suna da muhimmiyar rawa, amma wasu suna amfani da dandalinsu ta hanyar yaɗa bidiyoyi masu tayar da hankali na waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane, wanda hakan ba ya taimaka wa ƙoƙarin da muke yi tare,” in ji gwamnan.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa bayar da rahotanni cikin kula da hakki da ƙa’idojin aikin jarida na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa ayyukan tsaro, kare martabar waɗanda abin ya shafa, da kuma tallafa wa iyalan da ke cikin halin ƙunci.

By ukarofi

Leave a Reply