28
Aug
Rajistar haihuwa da mutuwa ba wani aiki ne na tattara alƙaluma kawai ba. Ita ce ginshiƙin da ƙasa ta zamani ke dogaro da shi wajen fahimtar al’ummarta, tsara buƙatunsu da kuma auna ci gabanta. Idan babu sahihan bayanan haihuwa da mutuwa, hasashen yawan jama’a yana zama cikin rashin tabbas, shirye-shiryen samar da ayyukan more rayuwa su raunana, yayin da manufofin ci gaba ke fuskantar haɗarin ginuwa a kan zato maimakon sahihan bayanai. Saboda haka, ci gaba da gazawar Nijeriya wajen yin rajistar haihuwa da mutuwa abu ne da ya kamata ya damu kowace matakin gwamnati. Binciken Alƙaluman Jama’a da Lafiyar…
